An ceto 'yar Najeriya da aka tallata a Facebook a Lebanon

Asalin hoton, Getty Images
An ceto wata 'yar Najeriya da aka sanya hotonta a shafin Facebook cewa ana neman mai sayenta a kasar Lebanon, kwanaki kalilan bayan hukumomin kasar ta Lebanon sun kama wani mutum da ake zargi da yunkurin sayar da matar.
Tallan matar ya janyo korafe-korafe da dama a shafukan intanet a Najeriya.
Hukumomin Najeriya sun ce ga alama dokar kulle da gwamnatin Lebanon ta kafa domin yaki da cutar korona ta saukaka gano matar da kuma mutumin da ake zargi da shirin sayar da ita.
Shugabar hukumar 'yan Najeriya mazauna kasashen waje Abike Dabiri-Erewa, ta shaida wa BBC cewa yanzu matar mai shekara 30 ta tsira kuma tana ofishin jakadancin Najeriya a Beirut bayan hukumomin Lebonan sun cetot ta.
Misis Abike Dabiri-Erewa ba ta bayyana yadda aka ceto matar ba, amma ta ce dokar hana zirga-zirga da hukumomin kasar suka kafa ta matakin yaki da cutar korona ya taimaka wajen gano inda matar take.
An kama mutumin ne a makon jiya wanda ake zargi da dora hoton wata 'yar Najeriya da ke aikatau a shafinsa na Faceebok domin sayar da ita kan dala 1,000, kwatankwacin naira dubu 370,000.
Ya makala hoton matar a jikin tallan da ya wallafa, wanda hakan ya janyo Allah-wadai a kafafen sada zumunta.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban manya da kakanan mata daga Najeriya da wasu sassan Afrika ake safararsu duk shekara zuwa kasashen waje.
Ta ce ana yawan rudarsu ne da alkawarin aiki a Turai da Asiya - amma a karshe sai su kare da aikatau ko kuma a tilasta musu yin karuwanci.











