Coronavirus: Wanne tasiri karyewar farashin man fetur zai yi ga Najeriya?

Farashin man fetur ya yi faduwar da bai taba yin irinta ba a cikin shekaru sakamakon annobar korona, lamarin da ya kara tayar da hankalin kasashen duniya.
Farashin danyen mai nau'in West Texas Intermediate na Amurka a ranar Litinin ya yi karyewar da ya zama tamkar ana neman kai da shi karon farko a tarihi.
Hakan na nufin masu samar da man suna biyan dillalai su karbi man daga hannayensu bisa fargaba rashin isasshen wurin da za su ajiye shi a watan Mayu mai zuwa.
Haka ma farashin danyen mai a Turai da sauran kasashen duniya ya fadi da kashi 8.9% inda ake sayar da man kan $26 duk ganga.
Yawan man fetur shi ne ya janyo faduwar farashinsa kamar yadda ta taba faruwa a 2015 inda farashin ya yi matukar faduwa
A halin yanzu dai akwai man da yawa a kasuwa, yayin da farashin ke faduwa saboda barkewar annobar coronavirus.
Kasuwar man ta bushe, bukatarsa kuma ta ragu, yayin da al'ummar duniya ta kasance kusan a kulle ba fita.
Ana fargabar cewa abin da ya janyo farashin danyen man Amurka faduwa babbar barazana ce ga sauran kasashe, domin abin da ya ci Doma ba ya barin Awai.


A farkon watan Afrilu mambobin kungiyar kasashe masu arzikin fetur OPEC suka amince su rage yawan man fetur da suke samarwa da kashi 10% - wanda shi ne adadi mafi yawa da aka taba ragewa na yawan man da ake fitarwa kasuwa.
Jaridar Bloomberg ta ce 'yan kasuwa a yammacin Afrika sun ce kusan ganga miliyan 10 ne yake jibge ba a sayar ba a watan Afrilu, yayin da watan ke dab da karewa.
Kuma yawancin man na Najeriya ne maimakon Angola, saboda kasashen Turai da suka saba saya sun daina saboda raguwar bukatarsa a kasuwa.
Farashin ya yi kasa fiye da farashin da Najeriya ta yi hasashe a cikin kasafin kudinta na bana.
Najeriya na dogaro ne da arzikin man fetur, kimanin kashi 90% na kudaden shigarta ke fitowa daga man da take sayarwa.

Tasirin faduwar maiga Najeriya
Faduwar farashin ne ya tilatstawa gwamnatin Najeriya sake tsara kasafin kudinta, inda a watan Maris gwamnatin Najeriya ta yi wa kasafin kudinta kwaskwarima saboda barazanar cutar korona.
Gwamnati ta rage sama da Naira biliyan N320 a kasafin kudinta na 2020, inda ya koma N10.27 tiriliyon kan dala 30 duk gangar mai daya, sabanin adadin da majalisa ta amince na dala 57 duk ganga.
Masana na ganin kasashen da ke dogaro da man fetur kamar Najeriya za su shiga mayuwacin hali, saboda raguwar bukatar man saboda annoba ta tilasta wa kamfanoni masu bukatarsa, rufe harkokinsu.
Farfesa Mustapha Muktar masanin tattalin arziki a Jami'ar Bayero Kano, ya ce yadda farashin man ke faduwa, gwamnatin Najeriya ba za ta iya aiwatar da kasafin kudin bana ba.
"Idan an sayar da mai yakan dauki lokaci kafin kudinsa ya dawo, nan gaba kasashen masu fetur za su shiga mugun mawuyacin hali saboda kudaden da suke samu ya ragu," in ji masani.
"Kudin da za a saya a kasuwar duniya ba zai kai kudin da aka hako shi ba," a cewarsa.
Ya kuma ce faduwar farashin zai yi tasiri sosai ga sauran fannonin tattalin arziki inda wasu ma za su durkushe, saboda arzikin mai ne ke samar da kudaden shiga da ke yunkura sauran fannonin.
"Idan farashin ya ci gaba da faduwa sauran fannonin ma za su durkushe," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Masanin ya ce a wannan lokaci na annoba ba wata dama ta saita tattalin arziki ga kasar da ke dogaro da man fetur.
Kamata ya yi gwamnati a yanzu ta fara tunanin tsuke bakin aljihu ya kasance sai abubuwan da suka zama dole kamar kula da lafiya da tsaro za ta kashe kudadenta a kai.
Duk wani abin da ba dole ba ga 'yan kasa to wajibi ne gwamnati ta rage, gwamnati ta san abubuwan da ba na dole ba domin kaucewa shiga mayuwacin hali.
Tsuke bakin aljihun shi ne matakin da ya kamata gwamnati ta dauka. a ririta kudaden da ake samu wajen harkokin kula da lafiya da tsaro da sauran abubuwa na dole.
Wasu na ganin faduwar farashin zai sa farashinsa a gidajen mai ya ragu, amma kuma zai rage yawan kudaden shiga da gwamnati ke samu.
Za a iya samun raguwar kudin sufuri wanda zai janyo raguwar kudaden kayayyaki da kuma raguwar hauhawan farashin kayyakin.
Sai dai Farfesa Mustapha ya ce rashin rage farashin iskar gas da kalanzir da sauran albarkatu da ake samu idan an tace danyen mai ba zai rage farashin kayayyaki ba.











