Najeriya za ta rage man fetur da take hakowa

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Najeriya ta bayyana cewa ta bi sahun kasashn kungiyar OPEC masu arzikin man fetur wajen rage adadin man da take hakowa a kowacce rana domin taimakawa wajen habaka farashinsa a kasuwar duniya.
Karamin ministan man fetur a kasar, Timipre Sylva ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a.
Ministan ya ce daga yanzu Najeriya za ta rika hako gangar mai miliyan 1.412 a kowacce rana da miliyan 1.495 da miliyan 1.579 a tsakanin watannin Mayu zuwa Yuni, Yuli zuwa Disamba da kuma Janairun 2021 zuwa Afrilun 2022.
Har wa yau, Najeriya ta bayyana fatanta cewa "idan abin ya dore" farashin man zai karu da akalla dala 15 a kan yadda yake a yanzu.
Bisa kiyasin hako danyen mai na Oktoban 2018, a yanzu Najeriya na hako ganga miliyan 1.829 a kowacce rana.
Wannan ragin ya biyo bayan yarjejeniyar da kasashen na OPEC tare da wasu kasashe masu arzikin fetur na rage ganga miliyan 10 na adadin da suke hakowa a kullum a yunkurinsu na farfado da darajar man.
Sai dai har yanzu yarjejeniyar ba ta kullu ba sakamakon jinkirin da kasar Mexico ta yi na saka hannu a kanta.
"Muna fatan idan wannan yarjejeniyar mai dumbin tarihi ta tabbata za a samu karuwar farashin mai da akalla dala 15 kan kowacce ganga a nan kusa," in ji Timipre Sylva.











