Coronavirus: NNPC ya tara wa Nigeria tallafin biliyan ₦21

Asalin hoton, @MKKyari
Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce ya tara tallafi na kusan naira biliyan 21 da zai bai wa gwamnatin Najeriya domin yaki da annobar coronavirus.
Shugaban kamfanin Mele Kyari ne ya shaida wa Sashen Hausa na BBC hakan a ranar Asabar, inda ya ce sun tara kudin ne da hadin gwiwar kamfanoni abokan huldarsu.
Mele Kyari ya ce sun bai wa gwamnati asibiti guda biyu domin kula da marasa lafiya. Guda daya yana unguwar Utako da kuma wani a Maitama.
A makon da ya gabata ne kamfanin, wanda mallakar gwamnatin tarayyar Najeriya ne, ya ce zai bai wa kasar tallafin naira biliyan 11.


Sai dai Mele Kyari ya ce yanzu adadin kudin ya karu sannan kuma akwai wasu kayan tallafin da ba kudi ba.
"Mun bayar da tallfin ne domin mu gwada wa gwamnati irin kokarinmu da mu da kamfanonin da ke hakowa da sayar da mai sannan kuma mu tallafa wa halin da muka shiga," in ji Mele Kyari.
Ya kara da cewa: "A makon da ya gabata muka ce za mu bayar da biliyan 11 amma yanzu adadin ya kai biliyan 21, wanda dukkanmu za mu bayar.
"Kamar yadda muka saba yin aiki a wannan fannin, kowa zai sayo kaya ne ya kawo, ba za mu karbi kobon kowa ba. Za mu fada wa mutane irin abin da muke so su sayo su kawo.
"Ko a yau ma mun samu motocin daukar marasa lafiya guda biyar kuma duk sati za mu dinga fada wa mutane abin da aka samu."
Zuwa yanzu mutum 209 ne suka kamu da coronavirus a Najeriya. Daga cikin wannan adadi, an sallami 25 sannan hudu sun mutu.











