Muhimman abubuwa guda biyar na jawabin Buhari

BBC

Jawabin Shugaba Muhammadu Buhari na daren Litinin ya zo ne bayan karewar wa'adin kulle tsawon mako biyu kan jihohin Lagos da Ogun da kuma babban birnin tarayya a kokarin yaki da cutar korona.

Alkaluma hukumomi sun ce a ranar Litinin 27 ga wata cutar wadda ta shiga cikin jiha 32 da kuma Abuja, babban birnin kasar, ta kashe mutum 40.

A cikin sabbin matakan da shugaban kasar ya bayyana akwai wasu muhimmai kamar haka:

Kulle jihar Kano

Shugaba Buhari ya ce dangane da Kano. "Na ba da umarnin tilasta rufe Kano gaba daya tsawon mako biyu, hakan kuma na farawa ne daga nan take.

Gwamnatin tarayya za ta tura dukkan mutanen da kayayyaki da suka wajaba don tallafa wa jihar wajen shawo kai da killace annobar da ma kare jihohi makwabtanta daga kasadar sake bazuwar cuta."Muhammadu Buhari ya ce yayin da suke ci gaba da kaifafa kokarin kai dauki a cibiyoyin jihar Legas da ma na babban birnin tarayya, ya kuma damu kan munanan al'amuran da ke faruwa a Kano cikin 'yan kwanakin nan.

A cewarsa: "Duk da ana ci gaba da gudanar da zuzzurfan bincike, amma sun cimma shawarar tura karin ma'aikata da kayan aiki da tallafin kwararru don karfafawa da mara baya ga kokarin gwamnatin jihar nan take."

Ya ce Kano, da ma sauran jihohi da dama da ake samun sabbin masu kamuwa da cutar korona, binciken farko-farko ya nuna cewa irin wadannan mutane galibi sun kamu ne sakamakon tafiya daga wata jiha zuwa wata da kuma yaduwar cutar a tsakanin al'umma da ke karuwa.

Dokar hana fitar dare a fadin kasa

Shugaba Buhari ya kuma ce a sauran jihohin kasar kuma, za a sanya dokar hana fitar dare daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe.

"Hakan na nufin an hana dukkan zirga-zirga a wannan lokaci sai dai fa ga masu ayyukan tilas," in ji Shugaba Buhari.

Tsawaita matakin kulle a Abuja, Lagos da Ogun

Muhammadu Buhari ya ce bisa la'akari da wasu batutuwa da suka gabata da kuma shawarwarin kwamitin shugaban kasa mai yaki da KOBID-19, kwamitocin gwamnatin tarayya su yi bita kan harkokin tattalin arziki da kuma kungiyar gwamnonin Najeriya.

Don haka: "Na amince da sassauta matakan kulle Abuja da Lagos da kuma jihar Ogun sannu a hankali kuma daki-daki, farawa daga ranar 4 ga watan Mayun 2020."

Ya ce don gudun wata tababa, matakin kullen a Abuja da Lagos da jihar Ogun zai ci gaba da kasancewa har wadannan sabbin matakai da gwamnatinsa ta dauka su fara aiki.

@NCDCgov

Asalin hoton, @NCDCgov

Takunkumi

Yayin jawabinsa, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce za su ci gaba da tabbatar da ganin ana amfani da takunkumi ko abin rufe fuska a bainar jama'a da kuma ci gaba da ba da tazara da tsaftar jiki.

Haka zalika ya ce tarnakin da aka sanya kan tarukan jama'a da na addinai suna nan daram.

Shugaban ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi da kamfanoni da masu zuciyar taimakawa jama.a su tallafa wajen samar da takunkuman ga al'ummar kasa.

Hana tafiye-tafiye a tsakanin jihohi

Muhammadu Buhari ya kuma sanar da hana duk wasu tafiye-tafiyen fasinja da ba su zama tilas ba a tsakanin jihohi har sai an ji karin sanarwa ta gaba.A cewarsa: "Za mu bar takaitattun tafiye-tafiye don kai kayayyaki da ayyuka a tsakanin jihohi ta yadda samar da kaya da ayyuka ba za su samu tangardar isa ga jama'a ba."