Coronavirus: Mai shafin Twitter zai tallafa wa duniya da dala biliyan daya

Asalin hoton, Getty Images
Jack Dorsey, mai kamfanin Twitter da manjahar biyan kudi ta Square, ya ce zai ba da tallafin dala biliyan daya a kokarin da duniya ke yi wajen shawo kan annobar coronavirus.
A cewar Mista Dorsey, kudin tallafin kaso 28 cikin 100 ne na dukiyar da ya mallaka.
Ya bada wannan sanarwa ce a shafinsa na twiter, tare da wallafa cewa ''bukatu na sake karuwa cikin gaggawa''.
Mista Dorsey bai ba da takamaiman bayanai kan inda za a kashe ko tura kudin ba domin yakar Covid-19.
A Amurka akwai karancin na'urar ventilator da kayayyakin kare kai, sannan kasuwanci da dai-daikun mutane na cikin yanayin na ukubar koma bayan tattalin arziki.
Mista Dorsey, zai yi amfanin da kason da ya mallaka a kamfanin Square wajen ware wannan tallafi wanda za a raba ta gidauniyar Start Small.
Mutumin mai shekara 43 shi ne shugaban kamfanin Twitter da Square.
Ya ce zai yi amfani da kudin da ya mallaka a Square saboda kudin da ya mallaka a manhajar ya zarta na twitter.
Ya kuma kara da cewa a hankali zai sayar da hannayen jarinsa, wanda hakan zai yi tasiri kan darajar kamfanin da girmar tallafin.
Da zarar an shawo kan annobar Covid-19, sauran kudadden za a karkatar da su ga fannin lafiyar yara mata da ilimi da bincike kan kudadden shiga na duniya.

Asalin hoton, Twitter
A kashi na shida na sakon twitter da ya wallafa, Mista Dorsey ya ce yana son ya ba da tallafin ne a wurin da zai ga tasirinsu a tsawon rayuwarsa.
Tallafin zai bi ta hannun kamfanin mai zaman kansa.
Wannan wata hanyar ce da masu arziki kan bi wajen ba da tallafi, sai dai ana yawaita sukar wannan salo da ake zargin ba bu adalci.
Mista Dorsey ya wallafa adireshi google, google doc da ya ce zai yi amfani da shi wajen bin sawun yadda ake kashe kudaden tallafin.
Shugaban kamfanin na twitter ba shi ne attajiri na farko da ke bayar da gudunmawar yakar wannan annoba ba.
Mai kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg, shi ma ya bada tallafin $30m, wanda ya ce za a yi amfanin da zunzurutunsu wajen neman magani.
Shi ma mai Amazon Jeff Bezos, ya bada tallafin $100m domin sayen abinci a Amurka don taimakawa wadanda ke fama da yunwa a wannan lokaci.
Kamfanin Apple a cewarsa shugabansa Tim Cook, za su bada gudunmawa domin kai kayayyakin magani Italiya, kasar da annobar ta fi yi wa illa a duniya.












