Shugabanni G5 Sahel sun fara taro kan matsalar tsaro a yankin

Taron na zuwa ne kwanaki kadan bayan mutuwar sojojin Jamhuriyar Nijar guda 71 a Inates.
Bayanan hoto, Taron na zuwa ne kwanaki kadan bayan mutuwar sojojin Jamhuriyar Nijar guda 71 a Inates.

Shugabannin kasashen Yammacin Afirka guda biyar da ke yaki da masu da'awar jihadi sun fara taron samar da tsaro a yankin, a Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar.

Taron na zuwa ne kwanaki kadan bayan mutuwar sojojin Jamhuriyar Nijar guda 71 a wani kwanton baunar da mahara suka yi wa sansanin sojojin a Inates.

Shugaban Nijar Niger Mahamadou Issoufou ya karbi gawarwakin sojojin da suka rasu a ranar Juma'a

Asalin hoton, NIGER PRESIDENCY

Bayanan hoto, Niger President Mahamadou Issoufou received the bodies of the dead soldiers on Friday

Shugabannin Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Njair da Mauritania da Chad na kar fuskantar matsin lamba domin su magance matsalar tsaro da ta yi sanadiyar mutuwar soja fiye da 230 a yankin a cikin wata hudu.

Kafin fara tattaunawa kan matsalar ta tsaro, sai da shugabannin suka halarci addu'oin da aka gudanar a kusa da makabatar da aka binne sojojin Nijar da masu ikirarin jihadi suka kashe a iyakar kasar da Mali.

Hakan ya jawo hankali cewa duk da girke sojojin Faransa guda 4,000 yankin, har yanzu rundunar yankin na G5 Sahel ba su samu nasara ba.

An kafa rundunar G5 Sahel ne shekara hudu da suka wuce, lokacin da kusan dukkan hare-haren masu da'awar jihadin ana samunsu na Mali.

Zuwa yanzu hare-haren karu sosai zuwa wasu sassan yankin na.

Hakan na da nasaba da karancin kayan aiki da rashin isasshen tsaro a wurin dakarun kasashen biyar.