Ta leko ta koma ga sabbin sarakunan Yarabawa 21

Asalin hoton, Pulse
Babbar kotun jihar Oyo ta tube sarakuna 21 watanni 53 bayan da aka yi musu karin girma daga kananan sarakuna zuwa mukamin Oba.
Alkalin kotun mai shari'a A. Aderemi ya yanke hukuncin ne a ranar Talata cewa nadin sarakunan ya yi karo da tsarin sarautar gargajiyar jihar, inda ya ce sarakan su koma mukamansu na da.
Tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi ne dai ya nada sarakan a lokacin yana kan karaga a 2017 ya daga martabar Baale zuwa Oba.
A 2018 ne Rashidi Ladoja wanda tsohon gwamnan jihar ne a 2003 sannan kuma mai rike da sarautar gargajiya, ya kai maganar kotu yana kalubalantar nadin, inda kotun ta rusa su.
To sai dai gwamna Ajimobi ya daukaka kara kuma har ranar da ya bar karagar batun na gaban kotu.
Magajinsa, Seyi Makinde ya waiwayi batun inda kotu ta tunbuke sarakan.
To sai dai mai magana da yawun sarakan da kotun ta tube, Senator Lekan Balogun ya ce "Rawaninsu na Baale na nan tun da an bi ka'ida wajen ba su mukamin".
Ana yi wa sabbin sarakan 21 dai kallon kishiyoyi ga Olubadan na Ibadan, Oba Saliu Adetunji.











