An nada Jose Mourinho a matsayin kocin Tottenham

Asalin hoton, Getty Images
An nada Jose Mourinho a matsayin sabon kocin Tottenham inda ya maye gurbin Mauricio Pochettino wanda aka kora daga kan mukamin ranar Talata.
Tsohon kocin na Chelsea da Manchester United Mourinho ya sanya hannu kan kwantaragi zuwa karshen kakar wasa ta 2022-23.
"Ingancin tawagar da kuma makarantar koyar da 'yan wasan kungiyar sun burge ni," in ji dan kasar ta Portugal mai shekara 56.
"Yin aiki da wadannan 'yan wasan shi ne abin da ya fi jan hankalina."
Mamallakin Kungiyar Spurs Daniel Levy ya ce: "Samun Jose na nufin samun daya daga cikin kocin da suka yi nasara a tamaula."
Tottenham ta kai matakin wasan karshe na Gasar Zakarun Turai a kakar wasan bara karkashin Pochettino, amma Liverpool ta yi nasara a kanta da ci 2-0 a Madrid.
Kocin dan kasar Ajantina, wanda aka nada shi a watan Mayun 2014, bai ci kofi ko daya ba a lokacin da yake jagorantar kungiyar, wadda rabonta da yin wata nasara tun lokacin da ta lashe gasar League Cup a shekarar 2008.
Levy ya ce Mourinho "yana da kwarewa, kuma zai iya zaburar da tawagar kuma yana da lissafin cin wasanni."
"Ya samu martaba a duk wata kungiya da ya jagoranta. Mun yi amanna zai karawa 'yan wasan kwarin gwiwa," a cewarsa.










