An kama basarake a Kaduna kan zargin aiki da masu garkuwa
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta ce ta kama wani basarake a jihar bisa zarginsa da yin aiki da masu satar mutane don neman kudin fansa.
Basaraken dai na cikin mutum 39 da rundunar ta yi holinsu a yammacin jiya Alhamis.
Kaduna na cikin jihohin Najeriya da suka fi fama da matsalar masu satar mutane domin neman kudin fansa.
A baya-bayan nan ma sai da dangin wani shugaban makarantar firamare a yankin Birnin Gwari suka ce masu garkuwar sun kashe dan'uwansu duk da kudin fansar da suka harhada suka kai masu.
Nabila Muktar Uba ta tattauna da DSP Yakubu Sabo, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kaduna. Saurari hirar a kasa:

















