'Yan bindiga sun kona makarantu a Nijar

'Yan bindiga a Jamhuriyar Nijar sun cinna wa wasu makarantu wuta a jihar Tillabery, lamarin da ya jawo rufe makarantu da dama a yankin da yake karkashin dokar ta-baci.
'Yan bindigar sun zo ne a kan babura sannan suka cinna wa wasu azuzuwa wuta ba tare da sun ce wa kowa komai ba, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.
Sun fara kona makarantun boko ne a yankin Makulandi na jihar ta Tillabery, abin da ke nuna yadda harkar tsaro ke tabarbarewa a yankin.
A karshen makon jiya ma wasu mutanen da ba'a san ko su wane ne ba suka sa wuta ga makarantun garuruwan Kiki da Bomoanga mai nisan kilometer 20 daga arewa maso yammacin garin Makulandi.
Wani mazaunin yankin na Makulandi da bai yadda a bayyana sunansa ba ya shaida wa wakiliyar BBC Tchima Illa Issoufou halin da ake ciki bayan kona makarantun.
"Ana cikin halin dar-dar saboda magana ta gaskiya malamai da daliban makarantun da aka kona duk sun watse kowa ya yi ta kansa," in ji shi.
Sannan ya ce da ma malaman ba 'yan garin ba ne saboda haka sun koma garuruwansu yayin da su kuma dalibai ke zaune a gidajensu.
Wannan na zuwa ne kwana biyu bayan 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka yi awon gaba da magajin garin Kabalewa a yankin Diffa mai iyaka da jihar Borno a Najeriya.
Har yanzu Boko Haram na ci gaba da zama barazana a kasashen tafkin Chadi.
Rikicin kungiyar, ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane a Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar, yayin da wasu da dama suka rasa gidajensu.











