An sace Basarake a yankin Diffa na Nijar

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga Nijar sun ce wasu 'Yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun yi awon gaba da magajin garin Kabalewa a yankin Diffa mai iyaka da jihar Borno a Najeriya.
Wani mazauni yankin ya shaidawa BBC cewa an yi awon gaba da basaraken ne tare da mai dakinsa.
Ya ce an kai harin ne a cikin dare a ranar Asabar zuwa safiyar Lahadi.
Ya kuma ce 'yan bindiga guda shida ne suka abka gidan magajin garin suka tafi da shi kuma sun kashe mutum daya wanda suka zarga ya bayar da labari a hanyarsu ta fita garin Kabalewa.
Sai dai zuwa yanzu babu wata sanarwa da ta fito daga jami'an tsaro ko hukumomin Nijar game da al'amarin
Har yanzu Boko Haram na ci gaba da zama barazana a kasashen tafkin Chadi.
Rikicin kungiyar, ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane a Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar, yayin da wasu da dama suka rasa gidajensu.






