'Hare-harenmu na tarwatsa 'yan Boko Haram zuwa Afirka'

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta tare da dakarun rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta MNJTF sun tilasta wa mayakan Boko Haram ko ISWAP neman mafaka a yankin tafkin chadi.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin, Kanal Sagiru Musa, ta ce majiyoyi masu karfi sun fada mata da cewa hare-haren rundunar sun sa mayakan Boka Haram din barin yankin tafkin Chadin , zuwa wasu yankuna da ke Sudan da kuma jamhuriyar tsakiyar Afrika.
Sanarwar ta kuma yi ikikarin cewa hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar mayakan Boko Haram da dama tare da lalata makamansu, ko da yake rundunar ba ta bayyana yawan adadin mayakan da suka rasa rayukansu ba.
Sai dai ta ce sojojinta tare da na rundunar tsaro ta hadin gwiwa na sintiri a wadannan wurare kuma za su ci gaba da luguden wuta domin murkushe mayakan Boko Haram da ke kokarin tserewa daga yankin tafkin Chadi.
Rundunar ta kuma ce tuni aka sanar da kasashen da wannan lamari ya shafa domin su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.
Wannan sanarwa dai na zuwa ne bayan harin da mayakan Boko Haram suka yi kokarin kai wa Birnin Maiduguri a ranar Lahadin da ta gabata ko da yake sojojin kasar sun dakile shi.
Sai dai sojojin kasar sun sha ikikarin karya lagon mayakan Boko Haram amma duk da haka mayakan na cigaba da kai hare hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya da Kamaru da kuma jamhuriyar Nijar.







