Yadda Boko Haram ta yi wa sojoji kofar-rago a Borno

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni na cewa akalla sojojin Najeriya takwas ne suka mutu sannan da dama suka bazama cikin daji sakamakon wani kwantan-bauna da wasu da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka yi musu a kan titin Monguno zuwa Maiduguri ranar Juma'a da safe.
Wani mazaunin garin Marte wanda ya shaida wa BBC abin da ya gani da idanunsa ya ce "mun yi kiliya da motoci guda uku kirar TATA cike fal da sojoji a kusa da wani kauye ana kiran sa Gasarwa, inda suka fito daga garin Munguno mu kuma tamu motar tana shiga garin na Mungonan."
Ya kara da cewa "Shigarmu Munguno ba jimawa sai kawai muka ga motoci na shigar da gawar sojoji masu yawa cikin barikin soji na Mai Malari da ke garin na Munguno."
Bayan fitowarmu daga Munguno sojoji sun tsare mu sun bincika motarmu kafin su ba mu iznin wucewa. Da muka karasa Gasarwa dai-dai wurin da muka yi kiliya da su a lokacin da muke shiga Munguno sai muka sake ganin wadannan motocin guda uku kirar TATA an yi fata-fata da su kuma ba kowa a ciki.
Ina kyautata tsammanin daya daga cikin motocin bam ne ya tashi da ita."
Rahotanni sun ce baya ga kisan sojojin, maharan sun yi awon gaba da makamai masu yawa.
Sai dai kokarin jin ta bakin sojoji ya ci tura kasancewar duk lambobin masu magana da yawun sojin Najeriya ba sa tafiya.
Har kuma kawo yanzu, babu wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar dangane da al'amarin.
Wannan hari dai na zuwa ne kasa da mako biyu da kungiyar Boko Haram ta kai wasu hare-hare a garuruwan Konduga da Gubio da Magumeri na jihar Borno.
Rahotonni sun ce mayakan Boko Haram ne wadanda ke biyayya ga kungiyar IS wato ISWAP suka kai hare-haren.
An samu asarar rayuka da jikkata da ma asarar dukiya bayan da maharan suka cinna wa shaguna da gidaje da wasu gine-ginen gwamnati wuta.











