Jam'iyyar hamayya ta Renamo ta nemi a soke zaben Mozambique

Asalin hoton, AFP
Babbar jam'iyyar hamayya a Mozambique ta bukaci a soke zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar Talata saboda a cewarta, rikici da magudi su ne suka mamaye zaben.
Jam'iyyar Renamo ta zargi jam'iyya mai mulki, Frelimo da saba yarjejeniyar yin zabe cikin lumana da suka cimma a tsakaninsu.
Wata tawagar Kungiyar Turai da ta sa ido kan zaben ta ce an samu afkuwar rikici da fargaba sannan kuma ba a baiwa bangarorin biyu dama a zaben ba.
Kakakin jam'iyyar Frelimo ya yi watsi da kalaman na EU inda ya ce an gudanar da zaben yadda ya kamata ba tare da samun hargitsi ba.
Ana dai yi wa zaben kallon zakaran gwajin dafi kan yarjejeniyar zaman lafiyar da jam'iyyun suka kulla bayan shafe shekaru 16 ana gwabza yakin basasa sannan aka sake samun takun saka tsakaninsu daga shekarar 2003 zuwa 2016.
Sakamakon farko da ke fitowa da ga rumfunan zabe ya nuna shugaba Filipe Nyusi ne kan gaba a zaben da kusan kashi 70 cikin 100 na kuri'un.
Shi kuwa abokin hamayya, Ossufo Momade na jam'iyyar Renamo yana da kashi 25 cikin 100.
Babban sakataren jam'iyyar Renamo, Andre Magibiri ya yi fatali da sakamakon zaben da aka sanar yana mai cewa bai yi dai dai da fatan da al'ummar kasar suke yi ba.
Ya kara da cewa zaben cike yake da rikici da cin zarafi da zuba kuri'un da ba a tantance ba a akwatunan zabe da sauran kura-kurai.
Sai dai jami'an hukumar zaben kasar sun karyata rahotannin cika akwatunan zaben da kuri'un karya.
Kimanin mutum 10 ne aka kashe sakamakon rikicin da ya biyo bayan zaben, a cewar wani mai sa ido kan yadda zaben ya gudana a kasar.
A baya bayannan an tsinci gawar wata jami'ar jam'iyyar Renamo da alamar harbin bindiga tare da ita da mai gidanta bayan da suka yi batan dabo a ranar zabe, kamar yadda Zenaida Machado, mai aiki a kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta shaida.
Kwanaki biyar kafin zuwan ranar zaben ma, an harbe wani mai sa ido kan zaben wanda ake zargin wata kungiyar 'yan sanda da yi.
'Yan sanda sun ce suna binciken abin da ya haddasa harbe Anastacio Matavel.











