Mozambique na 'matukar bukatar kayan agaji'

Neighbours chat while sitting in a flooded street of the Paquite district of Pemba. Wasu makwabtan juna kenan a lokacin da suke hira a wani titin da aka yi ambaliyar ruwa da ke lardin Paquite na Pemba.

Asalin hoton, AFP

Kasar Mozambique na bukatar agaji cikin gaggawa domin magance matsalolin da ake fuskanta bayan da mahaukaciyar guguwar Kenneth ta afka wa yankin, a cewar wata kungiyar ba da agaji.

Kungiyar Save The Children ta ce ayyukan agaji na fuskantar barazana kuma ana bukatar karin kudi.

Majalisar Dinkin Duniya ta bai wa Mozambique da kuma tsibirin Comoros dala miliyan 13 don samar da abinci da ruwa da kuma gyaran ababen more rayuwa.

Adadin wadanda suka rasa rayukansu a yayin guguwar da ta afka wa arewacin Mozambique ya kai 38, amma ana tunanin cewa zai karu, a cewar jami'ai a kasar.

A halin yanzu, masu aikin ceto suna kokarin isa yankunan da guguwar ta fi shafa.

Guguwar ta shafi kasar da ke kudancin nahiyar Afirka cikin makon da ya gabata da karfin iska mai tafiyar kilomita 220 a sa'a guda, a inda ta lalata dubban gidaje.

Ana kiyasta ce wa kasar za ta fuskanci ruwan sama fiye da yadda ta fuskanta a lokacin da guguwar Idai ta afka wa kasar a cikin watan bara, inda mutum fiye da 900 suka rasa rayukansu a Kudancin Mozambique da Malawi da kuma Zimbabwe.

Mai ake ciki a halin yanzu?

Masu aikin ceto sun yi ta kokarin kai kayan abinci da kuma magunguna zuwa yankunan da aka kasa isa saboda ambaliyar ruwa kafin a kara yin ruwan sama a ranar Talata.

Nicholas Finney, shugaban kungiyar Save The Children ya ce abin ya fi shafar mutane marasa galihu da ke zama a yankin.

''Wadanda ke fama da talauci a da, yanzu ba su da waniduniyar nan. A yayin da kyaututukan da ake bayar wa suka fara rayuwa, muna fuskantar mawuyacin hali,'' a cewar shi.

A cewar hukumar da ke kula da bala'o'i (INGC) ta Mozambique, mutum 38 suka rasa rayukansu sakamakon mahaukaciyar guguwar Kenneth, a yayin da kuma gidaje 35,000 suka lalace.

Har yanzu gwamnatin kasar ba ta san adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba tukuna.