An girke jami'an tsaro yayin zabe a Afghanistan

Bayanan bidiyo, Malaman zabe a kasar sun ce wadanda aka tantance da na'urar tantance masu kada kuri'a ne kadai za su jefa kuri'a a zaben.

An bude rumfunan zabe a Afghanistan domin kada kuri'a a zaben shugaban kasa.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin kasar ta girke jami'an tsaro masu dumbin yawa domin fargabar irin barazanar da 'yan kungiyar Taliban ke yi.

An bayyana cewa an baza sama da jami'an tsaro dubu 70 a fadin kasar domin dakile hare-haren 'yan Taliban wadanda suka sha alwashin kai wa a rumfunan zabe a kasar.

Zaben wanda aka daga har sau biyu na zuwa ne bayan tattaunawar zaman lafiya da ake yi tsakanin 'yan kungiyar ta Taliban da kuma Amurka ta wargaje a farkon wannan watan.

Manyan 'yan takaran da za su fafata a zaben sun hada da Ashraf Gani da kuma Abdullah Abdullah.

Dukkansu biyu sun mulki kasar a matsayin gwamnatin hadin guiwa tun 2014.

Jim kadan bayan fara kada kuri'a a kasar, an samu fashewar bam a kusa da wata rumfar zabe a kudancin birnin Kandahar inda a kalla mutane 16 suka samu raunuka.

Mai magana da yawun hukumar zaben kasar Zabi Sadaat ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ''an fara zabe a dukkanin rumfunan zaben kasar, kuma munji dadi kwarai da cewa mutane sun fara bin layi domin kada kuri'arsu.''

Ana sa ran mutane kalilan ne za su fita zuwa rumfunan zaben amma wata mai kada kuri'a ta shaida cewa a shirye take ta shafe sa'o'i da dama kan layi domin kada kuri'arta.

Reuters

Asalin hoton, Reuters

Me ya sa zaben Afghanistan ke da muhimmanci?

Sabon zababben shugaban kasar zai jagoranci kasar da ta shafe shekaru 40 cikin hali irin na yaki.

Rikici a Afghanistan na ci gaba da kashe dubban mutane a duk shekara kuma yana ci gaba da jawo sojoji daga sauran kasashe domin zuwa kwantar da tarzoma a kasar.

Kusan shekaru 20 kenan tun bayan da kasashen duniya suka sa baki a wannan yaki, Amurka na ta kokari wajen tattaunawa da 'yan Taliban domin yin yarjejeniya da su don kawo karshen yakin.

A halin yanzu Amurka na da sojoji kusan dubu 14 a Afghanistan hakazalika akwai wasu dubbai daga kasashe kamar su Birtaniya da Jamus da Italiya.

Wadannan sojojin na can ne domin horaswa da bada shawarwari ga sojojin kasar da kuma taimaka wa kasar wajen kawo karshen yakin da ya addabeta.

Duk wanda aka zaba a matsayin shugaban kasar na da jan aiki a gabansa ganin irin halin da kasar ke ciki a halin yanzu.