Dakarun Syria na tunkarar inda sojojin Turkiyya suke

Asalin hoton, AFP
Sojojin Syria sun fara isa ga arewacin kasar 'yan awanni bayan da gwamnatin kasar ta amince ta taimaka wa Kurdawan domin tunkarar dakarun Turkiyya.
Kafafan watsa labaran Syria sun ce dakarun gwamnati sun shiga Ain Issa, mai nisan kilomita 30 kudu da iyakar Turkiyya.
Yarjejeniyar dai na zuwa ne bayan da Amurka wadda ita ce babbar kawar Kurdawa ta ce janye ragowar dakarunta daga arewacin Syria.
Turkiyya ta fara kai hare-hare a arewacin na Syria da manufar fatattakar sojojin Kurdawa daga kan iyakar Syria.
A karshen mako ne dai Turkiyya ta yi ruwan bama-bamai a yankin da dakarun na Kurdawa suke da suka hada da Ras al-Ain da Tal Abyad.
An kashe gomman fararen hula sannan an kashe dakarun bangarorin biyu.
Amurka ta sanar ranar Lahadi cewa tana shirin kwashe ragowar sojojinta guda 1000 daga arewacin Syria.
Yarjejeniya tsakanin Syria da Kurdawa
Gwamnatin kurdawa da ke arewacin Syria ta sanar da cewa ta cimma yarjejeniya tsakaninta da sojojin kasar Syria domin tunkarar dakarun Turkiyya da ke kai musu hare-hare.
Yanzu dai sojojin na Syria ba za su shiga Tal Abyad ko Ras al-Ain, inda nan ne Turkiyyar ke cin karenta babu babbaka.
Shugabannin Kurdawan dai sun kafe kai da fata cewa su ne ke da iko a yankunan.











