Man U na son sayen Mandzukic, Rakitic zai bar Barca

Asalin hoton, Getty Images
Kulob din Tottenham na shirin cigaba da zawarcin dan wasan tsakiya na Sporting Lisbon. Bruno Fernandez.
Tottenham din dai ta kuduri sake neman dan wasan ne mai shekaru 25 da zarar an bude kasuwar musayar 'yan wasa a watan Janairu. (A Bola - in Portuguese)
Manchester United za ta kashe fam miliyan 10 wurin sayen dan wasan gaban Crotia, Mario Mandzukic daga Juventus a kakar wasanni mai zuwa. (Express)
Mandzukic mai shekaru 33 tuni ya cimma yarjejeniyar baka da kungiyar.
Barcelona ta zabi ta sayo dan gaban kulob din Paris St-German, Kylian Mbappe da kuma Harry Kane na kulob din Tottenham da ke Ingila a kan dan wasan Liverpool, Roberto Firmino. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Wakilin dan wasan tsakiyar Chelsea Jorginho ya ce akwai yiwuwar zai iya komawa gasar Serie A ta Italiya, don cigaba da buga tamaula.(Radio Sportiva - in Italian)
A wata mai kama da haka Olivier Giroud ya ki ya soki mai horar da yan wasan Chelse Frank Lampard. To sai dai dan wasan mai shekaru 33 ya ce ba zai amince da cigaba da rashin sashi a wasanni ba. (Le Pelerin, via Star)
Kulob din Barcelona na shirin sayar da dan wasan tsakiya Ivan Rakitic a watan Janairu inda ake tunanin Manchester United za ta taya dan wasan. (Sport - in Spanish)
Cigaba da zawarcin da kulob din Real Madrid ke yi na dan wasan tsakiyar Tottenham Christian Eriksen mai shekaru 27, zai ta'allaka ne kan yadda lamurra ke gudana a kulob din nasa.(AS)
A wata mai kama da haka, Eriksen din zai fi son ya kulla yarjejeniya da Real Madrid a kakar wasannin badi a maimakon watan Janairu. (Express)
Dan wasan tsakiyar Ingila Declan Rice ya ce yana jin dadin zama da kulob dinsa West Ham, ya kuma bayyana jita-jitar cewa zai koma Man U da buga wasa a matsayin wani labarin kanzon kurege.(Mirror)
Shugaban kulob din Bayern Munich ya ce ba ya tunanin dan wasan gaba Thomas Muller mai shekaru 30 zai bar kungiyar duk da rahotannin da ke cewa dan wasan ba ya jin dadin zama a kungiyar. (Express)
Tsohon mai horas da yan wasan Tottenham Harry Redknapp ya ce ba ya jin Tottenham za ta iya korar kociyanta Mauricio Pochettino,inda ya ce yan wasan Pochettino ba su da bambanci da na kulob din Liverpool ko Manchester City. (Mail)
Dan wasan tsakiyar Kenya da ke wasa a Tottenham Victor Wanyama na sa ran sake komawa tsohon kulob dinsa wato Celtic, bayan da komawarsa kungiyar Club Bruges ba ta yiwu ba.. (Football.London)











