Ko kun san me ake tattaunawa a taron Majalisar Dinkin Duniya?

Asalin hoton, Getty Images
Batun ci gaban ƙasashen duniya da kuma yaƙi da sauyin yanayi za su zama gaba-gaba a cikin abubuwan da za a tattauna lokacin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a birnin New York.
Haka nan ma akwai yiwuwar batun samamen da Rasha ke yi a Ukraine ya zama babban batu.
Mece ce Majalisar Dinkin Duniya?
Majalisar Dinkin Duniya kungiya ce ta kasashe 193 da aka kafa bayan karkare yakin duniya na biyu a 1945, da manufar wanzar da zaman lafiya tsakanin kasashen duniya.
Shi kuma babban taron Majalaisar Dinkin Duniya wato General Assembly (UNGA) na daya daga cikin zauruka guda shida na majalisar kuma a taron ne ake hakkake abubuwan da Majalisar ta Dinkin Duniya za ta gudanar.
Taron na General Assembly shi ne wanda yake hada kasashen 193 a wuri guda a kowane watan Satumba.
Me za a tattauna?

Asalin hoton, Getty Images/ED JONES
Tatattaunawa kan tabbatar da muradun ƙarni za ta gudana ne tsakanin 18 zuwa 19 ga wata, inda ƙasashe za su tattauna kan ƙudurin Najalisar Ɗinkin Duniya na "tabbatar da muradun ƙarni."
Wannan sun ƙunshi kawo ƙarshen yunwa da talauci a duniya, da bunƙasa kuɗaɗen shiga da ilimi a faɗin duniya, da bunƙasa samar da tsaftataccen ruwa da tsaftar muhalli.
Babbar tattaunawar za ta gudana ne daga 19 zuwa 23 ga watan Satumba, kuma a ci gaba da shi a ranar 29 ga watan na Satumba.
A lokacin wannan tattaunawa wakilan dukkanin ƙasashe masu wakilci a Majalisar ta Dinkin Duniya za su yi bayani kan abubuwan da suke damun su.
Taron ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi zai gudana ne a ranar 20 ga watan Satumba. Manufar taron shi ne haɓɓaka hanyoyin yaƙi da sauyin yanayi.
Akwai kuma taruka da aka shirya kan samar da kuɗi domin aiwatar da ci gaban tattalin arziƙi, da yaƙi da annoba da kuma kawar da makaman nukiliya.
Ana zaɓen shugaban babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ne a kowace shekara. A wannan shekarar, Dennis Francis, jami'in diflomasiyya daga Trinidad and Tobago shi ne ke riƙe da muƙamin.
Wace matsaya za a iya cimmawa?
Taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya wata dama ce ga shugabannin ƙasashe daga faɗin duniya su haɗu a wuri ɗaya.
Yawancin manyan manufofi da akan cimma na samuwa ne daga tarurruka da akan yi a gefen taron babban zauren majalisar.
Ana sa ran shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenski zai halarci taron kuma ya yi jawabi a kwamitin tsaro na Majalisar game da halin da ake ciki a ƙasar.
A ɓangare ɗaya kuma shugaban Rasha, Vladimir Putin, da na China Xi Jinping da na Faransa, Emmanuel Macron duk ba za su samu halartar taron ba. Haka nan wasu rahotanni na cewa firaministan Birtaniya, Rishi Sunak ma ba zai halarta ba.
Wadanne batutuwa ne za su shahara a labarai wannan makon?
Wasu daga cikin manyan batutuwan da za su mamaye kafafen watsa labarai su ne wadanda za a yi su a wajen zauren taron.
Boris Johnson na Birtaniya na halartar taron kuma hakan na nufin ka iya mayar da hankalinsa zuwa batutuwan da suka shafi ficewar kasarsa daga Tarayyar Turai.
A jajibirin taron na Majalisar Dinkin Duniya, an gudanar da wani taron koli kan sauyin yanayi a inda wata matashiya mai shekara 16, Greta Thunberg ta fada wa shugabannin duniya cewa "kun dakile min mafarkina da kuriciyata da jawabanku........ya ya aka yi haka?"
Firaministan India, Narendra Modi ya ce duniya ba ta yin abin da ya kamata kan sauyin yanayi.
"Abin da muke bukata shi ne sauyin halayya," inji Modi.
Ya taron yake gudana?

Asalin hoton, Getty Images
Bisa al'ada, shugaban kasar Brazil ne yake bude taro da jawabi ko kuma wakilinsa sannan sai shugaban kasa mai karbar bakunci wato Amurka.
Brazil ce ke fara jawabi kasancewar a lokacin da aka fara taron Brazil din ce take bugun kirji ta fara jawabi saboda kasashe ba sa son bugun kirji su fara jawabi. Daga nan ne kuma abin ya zama al'ada cewa Brazil ce take fara jawabi a taron.
A lokacin taron kowane shugaban kasa ko kuma wakilin kasa zai yi jawabi a cikin minti 15 duk da cewa wani lokaci wasu na wuce hakan.
Shugaban Cuba Fidel Castro ne mutumin da ya kafa tarihi inda ya yi jawabin nasa na awanni hudu da rabi a 1960.
Abubuwa masu jan hankali da suka faru a tarukan baya

Asalin hoton, Getty Images
A 2019, mai rajin kare muhalli ƴar asalin ƙasar Sweden, Greta Thunberg, ƴar shekara 16 a lokacin, ta ce wa shugabannin ƙasashen duniya "kun lalata min burukana da yarintata saboda rashin cika alƙawurranku. Don me kuke yin haka?"
A shekarar 2006, shugaban Venezuela, Hugo Chavez ya bayyana shugaban Amurka na wancan lokaci George W Bush da 'shaidani' yayin jawabi a taron.
Ya ce mumbarin da shugaba Bush ya tsaya ya yi magana "har yanzu yana warin sinadarin Sulphur".

Asalin hoton, Getty Images/STAN HONDA
Shekaru uku bayan nan kuma, tsohon shugaban Libya, Colonel Gaddafi ya kwashe fiye da awa daya yana jawabi inda har ya yi korafi dangane da yadda wakilan kasashe suke fita daga dakin taron.
Ya kuma zargi manyan kasashen duniya da saba dokokin da suka kafa Majalisar Dinkin Duniya, kafin daga bisani ya yi jifa da kwafin dokokin.
A 2017, Shugaba Donald Trump ya ce shugaba Kim Jong-un na Koriya ta Arewa na "kokarin kashe kansa da kansa".
An fara wallafawa 24 Satumba 2019, an sabunta 19 Satumba 2023.











