Majalisar Ɗinkin Duniya za ta fara aikin jin-ƙai a Sudan

Asalin hoton, Getty Images
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya zai tura wakili na musamman wanda zai tsara aikin jin-kai a Sudan yayin da rikicin da ake yi a kasar tsakanin bangarori biyu na soji ya shiga mako na uku.
Babban jami'in aikin jin-kai na Majalisar Martin Griffiths ya ce zai duba ya ga yadda za a samar da taimakon gaggawa ga miliyoyin 'yan Sudan, wadanda rayuwarsu ta shiga wani mummunan yanayi a lokaci daya.
Majalisar Dinkin Duniyar tare da Kungiyar Tarrayar Afirka, AU sun roki sojojin na Sudan da kuma dakarun RSF da ke yaki da juna da su mutunta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da suka ce za su bi a baya.
Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana aniyar tasa ne ta aikawa da babban jami’in aikin jinkai na majalisar Martin Griffiths Sudan din domin tallafa wa jama’ar da ke kasar wadanda suka samu kansu a wannan hali na tsaka-mai-wuya dare daya.
A wata sanarwa da kakakin Babban Sakataren Stephane Dujarric ya fitar ya ce, Mista Guterres ya dauki matakin ne ganin yadda al’amura ke kara tabarbarewa a kasar a sakamakon wannan rikici da ya shiga mako na uku.
Rikicin a tsakanin rundunar sojin kasar bisa jagorancin shugaban mulkin soja Janar Abdel Fattah al-Burhan da jagoran dakarun kar-ta-kwana na Rapid Support Forces, ko RSF, Janar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti.
Ana ganin shugaban na RSF ya zama hamshakin attajiri a shekarun baya bayan nan bayan da ya kama yankin Sudan da ke da arzikin zinare.
Kuma ana ganin rundunarsa na da mayaka da suka kai kusan dubu dari daya, da ake ganin su ke da iko yanzu da yawancin sassan babban birnin Khartoum.
Abin da ya ja sojoji ke harba musu makamai a yankunan da suke rike da su, tare da neman su mika wuya.
Sannan ana ganin fargabar rasa iko da dukiya ita ce babbar matsalar hana mutunta duk wata tattaunawar sulhu.
A sanarwar kakakin ya ce Mista Guterres ya nuna damuwar Majalisar kan abin da ya kira tabarbarewar al’amura cikin gaggawa da kuma girma a Sudan.
Bangarorin sojin biyu da ke yaki na zargin junansu da saba wata sabuwar yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta sa’o’i 72 da suka amince da ita, yayin da wadda suka yi a baya ta kawo karshe, wadda ita ma dai ba su mutunta ta ba sosai.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bangarorin na ci gaba da gwabza fada ba kakkautawa domin kama iko da babban birnin, Khartoum.
A dangane da hakan ne Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afirka, AU, tare da kungiyar kasashen yankin na Afirka ta Gabas, IGAD, suka fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa.
A sanarwar sun yi gargadin cewa al’ummar Sudan na cikin wani mawuyacin hali da ke matukar bukatar yarjejeniyar dakatar da bude wuta domin jin-kai.
Kungiyoyin uku suka ce dole ne wannan sabuwar yarjejeniya ta kai ga dakatar da bude wuta dindindin.
Sun kuma yi kira ga bangarorin da ke yaki da su daina kai hari kan yankunan da ke da tarin jama’a farar hula su kuma mutunta dokokin duniya.
Miliyoyin mutane ne wannan rikici ya rutsa da su a kasar inda wasu suka boye a cikin gidajensu, cikin hadari, a rashin samun hanyar ficewa daga kasar kamar yadda dubbai ke ci gaba da ficewa.
Musamman ta ruwa inda ake dibarsu a jiragen ruwa daga birnin Port Sudan na gabar teku zuwa birnin Jeddah na Saudiyya.
Sojojin Saudiyya sun ce zuwa yanzu sun tserad da mutane sama da dubu 500 na kasashe dari.
Abin da ya janyo yabo ga Saudiyyar daga jami’an diflomasiyya.











