Amurka ta kwashe ɗaruruwan ƴan ƙasarta daga Sudan

Aikin kwashe mutane daga Sudan

Asalin hoton, EPA

Kafofin watsa labarai na Amurka sun ce wani jerin-gwanon motocin bas-bas da ke dauke da Amurkawa farar hula 300 ya bar babban birnin Sudan Kahrtoum, inda ya nufi birnin Port Sudan na gabar teku, da ke da nisan kilomita 800 a gabashi.

Dakatar da bude wuta da bangarorin soji biyu da ke yaki da juna suka ayyana a Sudan din ba ta kankama ba ko ma a ce ba ta aiki.

Ana mummunan fada a babban birnin, Khartoum da kuma yankin Darfur na yammacin kasar.

Wannan kwashewar ta kasance kusan irinta mafi girma ta farko da aka yi, inda aka raba Amurkawa wadanda ba jami’an diflomasiyya ba ne da Sudan din domin tserad da su daga rikicin da ya barke tsakanin bangarorin sojin kasar biyu.

Bangaren babban hafsan rundunar soji kuma jagoran Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa da ke iko da dakarun Rapid Support Forces, RSF, Janar Hamdan Dagalo, a kan neman iko da kasar.

Kwana biyar da suka gabata ne aka kwashe jami’an diflomasiyya da sauran jami’ai na Amurkar daga kasar bayan barkewar wannan rikici tun ranar 15 ga watan Afirilun nan na 2023.

Rahotanni sun ce ana kwashe wadannan Amurkawan ne tare da tsaro da rakiyar kananan jiragen sama na yaki marassa matuka da ke sha’awagi a sama.

Kasashe da yawa na kammala aikin kwashe mutanensu, bayan da tuni suka fitar da dubbai.

Rahotanni daga tashar jiragen ruwa ta birnin Port Sudan inda za a kai mutanen na cewa wurin da jiragen ruwa ke tsayawa cike yake da daruruwan ‘yan kasar Yemen da ‘yan kasashen yankin tekun Fasha da ‘yan Syria wadanda ke jiran a kwashe su zuwa Saudi Arabia.