Yayin da ƙasashe ke rige-rigen kwashe mutanensu, wanne hali 'yan Sudan ke ciki?

Asalin hoton, Reuters
Ɓangarori biyu masu fafatawa da juna na dakarun tsaro a Sudan sun amince da sabunta yarjejeniyar tsagaita wuta tsawon kwana uku, jim kaɗan kafin wadda aka ƙulla ta kawo ƙarshe.
Ƙarin sa’a 72 – ya zo ne bayan yunƙurin diflomasiyya na ƙasashe makwabta da kuma Amurka, da Burtaniya a Majalisar Ɗinkin Duniya.
Amma ana ci gaba da ba da rahotannin gwabza ƙazamin faɗa a Khartoum babban birnin ƙasar.
Yarjejeniyar da aka ƙulla a baya, ta bai wa dubban mutane damar tserewa zuwa tudun-mun-tsira, a yayin da gomman ƙasashe suka yunƙura wajen kwashe mutanensu.
Faɗan wanda aka shafe kusan mako biyu ana gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da mayaƙan rundunar jami'ai masu kayan sarki ta RSF ya haddasa mutuwar ɗaruruwan mutane.
An sa rai, tsagaita wutar za ta kawo ƙarshe ne da misalin ƙarfe goma na safiyar Alhamis agogon GMT.
A yammacin Alhamis ne kuma, rundunar sojin Sudan ta amince da tsawaita lokacin tsagaita wutar, inda daga bisani ɗaya ɓangaren na ƙungiyar mayaƙan RSF su ma suka bi sahu.
Sudan ta Kudu ta yi tayin shirya zaman tattaunawa a ƙasarta, kuma rundunar sojin ta amince da aikewa da wakilai don hawa teburin tattaunawar.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce Washington ‘’ta yi aiki tuƙuru’’ don ganin an ƙara kwanakin tsagaita wutar, sannan ta yi nasara ganin an sassauta tashin hankalin.
Amma kuma daga bisani ne mai magana da yawun fadar White House Karine Jean-Pierre ta bayyana cewa halin da ake ciki faɗa na iya ƙara muni a kowanne lokaci.
Wanne hali mutanen Sudan ke ciki

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A halin yanzu, rundunar RSF da shaidu sun ce sojoji na ta luguden wuta a sansanonisu na birnin Khartoum.
Ministar harkokin waje a tsohuwar gwamnatin farar hula, Maryam al-Sadiq al-Mahdi, ta shaida wa BBC daga gidanta a birnin Khartoum cewa duk da tsagaita wutar, fararen hula na cikin zullumi.
"Abin da suka kira yarjejeniyar tsagaita wuta, ba ta da wata alaƙa da abubuwan da ke faruwa," ta ce. "Luguden wutar da jiragen yaƙi ke yi na faruwa kusan ba dare ba rana.’’
An kuma ba da rahoton ɓarkewar faɗa a gabashin yankin Darfur da sauran larduna.
Aƙalla mutum 512 ne aka halaka a fadan, sannan wasu 4,200 ne suka jikkata, ko da yake, yawan adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa matuƙa.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce tana tsammanin za a iya samun ƙarin mace-mace saboda ɓarkewar cutuka dalilin rashin harkokin kula da lafiya.
Jami’an lafiya sun ce akasarin asibitoci a yankunan da ake tashin hankalin ba sa aiki, sannan fiye da kashi 60 na asibitoci a birnin Khartoum ba sa aiki.
Shugaban kwamitin kula da ayyukan ceto na duniya, kuma tsohon sakataren wajen Burtaniya David Miliband, ya ce ƙasashen duniya na cikin hatsari game da halin ko-in-kula da tashin hankalin da ke daɗa ruruwa a Sudan, yayin da ake rige-rigen kwashe ‘yan ƙasashen waje.
"Ganin yadda a cikin kwana 10 duk rahotannin kafafen labarai da akasarin hankulan ‘yan siyasa da dama suka karkata wajen fitar da dubban mutane.
Amma ba a kan buƙatar da ke akwai ta kula da abubuwan da suka damu miliyoyin mutane ba,’’ in ji shi.
"Ko shakka babu, rayuwar dubban mutanen da ke buƙatar a kwashe su tana da muhimmanci, amma wanne hali mutane miliyan 45 da aka bari a baya ke ciki?
Sudan na da yawan jama'a miliyan 15 da ke buƙatar agaji, kuma ɗaya daga cikin kiran da muke yi yanzu a matsayinmu da ƙungiyar kula da ayyukan ceto ta duniya shi ne kada mu bari, mu auka cikin tarkon tunanin cewa da zarar an kwashe dubban mutane matsala ta kau".
Wata sanarwar rundunar sojin Sudan da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato ta ce dakarunta sun karɓe iko da akasarin yankunan ƙasar, amma "halin da ake ciki yana cike da sarƙaƙiya a wasu sassa na babban birnin ƙasar’’.
BBC ba ta iya tantance iƙirarin sojojin ba.
Ƙasashen waje, da suka hadar da Burtanita na ta yin kira ga mutanensu su fice daga Sudan cikin gaggawa.
Yayin da take jawabi ranar Alhamis da yamma, Mis Jean-Pierre ta yi kira ga Amurkawa su bar ƙasar cikin sa’a 24.
An ci gaba da kwashe mutane, amma ‘yan ƙasashen waje da dama har yanzu suna nan maƙale a Sudan.
Wasu sun yi ta ƙoƙarin kai wa ga ƙaramin filin jirgin saman da ake amfani da shi wajen kwashe mutanen.
Fararen hula ‘yan ƙasar na ci gaba da tserewa daga Kahrtoum, inda ake fama da matsalolin samun abinci, da ruwan sha da kuma man fetur.
Faɗan ya ɓarke ne ranar 15 ga watan Afrilu saboda zazzafar gwagwarmayar neman iko tsakanin sojojin Sudan da mayaƙan runduna masu kayan sarki ta RSF.











