Ɗaliban Najeriya sun fara baro Sudan domin dawowa gida

Asalin hoton, Nigerians in Diaspora Commission
Iyaye da dangin ɗaliban Najeriya masu karatu a Sudan da ta tsunduma cikin yaƙi, na can suna dakon labarin isar 'ya'yansu tudun-mun-tsira, bayan hukumomi sun fara aikin kwashe su a jiya Laraba.
Da misalin ƙarfe 5 na yamma agogon Najeriya ne sawun farko na motocin bas-bas - waɗanda rahotanni suka ce za su tafi cikin ayari - suka tashi daga birnin Khartoum ɗauke adadi mai yawa ɗaliban da 'yan asalin Najeriya.
Hukumomi ba su bayyana taƙamaimai adadin ɗaliban da aka fara kwashewa daga Sudan ɗin ba.
Sai dai a cikin dare kuma, bayanai sun ce motocin bas-bas sawu na biyu shi ma ya tashi zuwa ƙasar Masar.
Doguwar tafiya ce mai nisan kilomita 2,173.9 kuma bayanai suna cewa 'yan Najeriyan suna iya kwashe tsawon kwana biyu ko uku suna tafiya, kafin su isa birnin Alƙahira. Nisan tafiyar dai ya zarce daga Kano zuwa Lagos, sannan a sake komawa.
Gwamnatin Najeriya ta tsara cewa daga babban birnin Masar ne, inda ake sa ran ɗaliban za su isa a motoci, sannan kuma za a kwashe zuwa birnin Abuja ta jirgin sama.
Doguwar tafiya ce da za a shafe tsawon sa'a biyar da minti talatin da biyar ana yi.
Ana kyautata zaton akwai 'yan Najeriya fiye da 5,000 a Sudan da ke son a kwashe zuwa gida saboda yaƙi, a cikinsu 3,500 ɗalibai ne.
Za su yi tsawon sa'a 13 kafin su sauka a Wadi Halfa mai ratar kilomita 30 daga kan iyakar Masar, daga nan kuma su ƙarasa Aswan a cikin Misira.
Mai yiwuwa bayan sun huta ne kuma, za su sake ɗaukar hanya don yin wata tafiya ta tsawon sa'a 11 wadda za ta dangana da su birnin Alƙahira.
Dubban jama'a ne ke ci gaba da ficewa daga Sudan daidai lokacin da wata yarjejeniyar tsagaita ta tsawon sa'a 72 tangal-tangal, inda rahotanni ke cewa an ci gaba da jin rugugin bindigogi nan da can.
Hukumomin Masar sun ce aƙalla mutane fiye da dubu 10 ne suka tsallaka cikin ƙasar a tsawon kwana biyar tun bayan kaurewar faɗa tsakanin rundunar sojojin Sudan da mayaƙan rundunar masu kayan sarki ta RSF.
Wasu 'yan asalin Najeriya da suka shafe shaekaru da dama suna zaune a Sudan sun bi sahun ɗaliban ƙasar da suka je karatun jami'a a ƙoƙarinsu na kuɓuta daga faɗan da ake ci gaba da gwabzawa.
Wasu rahotanni na cewa nisan tafiyar 'yan Najeriyar zai iya ƙaruwa don kuwa da yiwuwar za su riƙa haɗuwa da sojoji da kuma jami'an tsaro masu bincike.

Motocin bas-bas kimanin arba'in da shida ne hukumomin Najeriya suka tanada don kwashe ɗaliban da ke son ficewa daga Sudan, in ji Muhammad Nura Bello, shugaban ƙungiyar dalibai 'yan Najeriya a Sudan International University.
Babban Daraktan Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) da jami'an ofishin Jakadancin Najeriya a Masar da Ethiopia ne za su tarbi ƴan Najeriyar da suka baro Sudan ta titin mota.
Abin da ya faru a aikin kwashe ƴan Najeriya
Shugaban ƙungiyar ɗalibai 'yan Najeriyar a jami'ar Sudan International University ya ce aikin kwashe ɗaliban ya zo a wani yanayi inda aka riƙa rige-rigen shiga motoci, wani lamari da ya yi yunƙurin haddasa kai ruwa rana.
A cewarsa, "ɗalibai kowa so yake ya tafi gida, a haka kuma akwai mazauna gari, waɗanda asalinsu ƴan Najeriya ne.
Kasancewar akwai ɓarkewar rigingimu da rashin tsaro, su ma suna son su wuce Najeriya", cewar shugaban ɗaliban.
"Samun labarin za a kwashe ƴan Najeriya zuwa gida, su ma kawai sai suka zo suka ce za su shiga, abin sai da ya kawo rigima tsakanin su da ɗalibai".

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Faɗa ya ɓarke ne tsakanin dakarun manyan janar-janar biyu na Sudan.
Abdel Fattah al-Burhan, jagoran rundunar sojojin Sudan da kuma Mohammed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da suna Hemedti, shugaban dakarun kai ɗaukin gaggawa don tallafawa ayyukan tsaro wato RSF.
Da farko, mutanen biyu sun yi aiki tare. Sun yi wani juyin mulki - inda suka riƙa goyon bayan juna - amma yanzu an gan su a rana, faɗan wa ya fi ƙarfi iko tsakaninsu, na durƙusar da Sudan.
Dukkansu sun ba da gagarumar gudunmawa wajen murƙushe rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya a kan 'yan tawayen Darfur, wani yaƙin basasa a yankin yammacin Sudan da ya fara a shekara ta 2003.
Janar al-Burhan ya sau ɗaukaka da ƙarin girma har ya kai matsayin karɓar iko da rundunar sojojin Sudan a Darfur.
Hemedti ya taɓa zama kwamandan ɗaya daga cikin rundunonin sojojin sa-kai na Larabawa masu yawa da ake kira Janjaweed, waɗanda gwamnati ta ɗauko kuma ta hanyoyi masu cike da rashin imani suka murƙushe ƙungiyoyin 'yan tawayen Darfur waɗanda ba Larabawa ba.











