Rikicin Sudan: Ana jin harbe-harbe duk da yarjejeniyar tsagaita wuta

Asalin hoton, Reuters
Da alamu yarjejeniyar tsagaita wuta Sudan tana ɗan aiki bayan an ayyana ta, da tsakar dare agogon ƙasar misalin ƙarfe 10n dare agogon GMT ranar Litinin.
Yunkuri na huɗu kenan da ake yi don tsagaita faɗan wanda aka fara ranar 15 ga watan Afrilu, sai dai a baya yarjejeniyar ba ta ɗore ba.
Sakataren wajen Amurka Antony Blinken ya ce an amince da yarjejeniyar tsagaita wuta tsawon sa'a 72 tsakanin sojojin Sudan da mayaƙa masu kayan sarki na rundunar (RSF) bayan shafe sa’a 48 ana tattaunawa.
An ba da rahoton jin amon harbe-barbe a Khartoum, babban birnin ƙasar ranar Talata.
Haka kuma an ba da rahotannin ganin shawagin jiragen yaƙi a sama, amma yanzu fararen hula sun koma gudanar da harkokinsu a titunan babban birnin.
Aƙalla mutum 459 aka kashe a rikicin ya zuwa yanzu, ko da yake ana jin cewa haƙiƙanin adadin na iya fin haka.
Duka ɓangarorin biyu da ke gwabza faɗa da juna, sun tabbatar da cewa za su sassauta.
Sai dai Tagreed Abdin, wadda ke zaune a wani wuri mai nisan kilomita bakwai daga tsakiyar Khartoum, ta ce tana jiyo amon roka daga gidanta a ranar Talata da safe duk da yarjejeniyar tsagaita wutar.
"Halin da ake ciki yanzu shi ne da safiyar nan, ana jin ƙarar harbin roka da buɗe wutae," kamar yadda ta faɗa wa BBC.
"Ga alama babu yarjejeniyar tsagaita wuta da ke aiki," ta ƙara da cewa.
Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres ya yi gargadin cewa tashin hankalin na Sudan, ka iya aukar da mummunan yanayi da zai ɗaiɗaita duka yankin da ma wasu wuraren.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun bayan fara tashin hankalin ne aka umarci mazauna birnin Khartoum su zauna a gidajensu, abin da ya janyo ƙarancin abinci da ruwan sha.
An yi luguden bama-bamai a kan muhimman ababen more rayuwa kamar bututan samar da ruwan sha, abin da ya tilasta wa mutane shan ruwan Kogin Nilu.
Ƙasashe suna ta rige-rigen kwashe jami’an diflomasiyyansu da fararen hula a yayin da faɗan ya ƙara rincaɓewa a tsakiyar yankunan birnin mai yawan jama'a.
Akwai fatan cewa tsagaita wutar za ta bai wa fararen hula damar ficewa daga birnin.
Su ma gwamnatocin ƙasashen waje na cike da fatan hakan zai ba su damar ci gaba da kwashe mutanensu daga cikin ƙasar.
Ma’aikatar wajen Masar ta bayyana a ranar Litinin cewa an hallaka wani jam’in diflomasiyya lokacin da yake tuƙa mota zuwa ofishin jakadancinsu a birnin Khartoum don taimaka wa aikin kwashe ‘yan ƙasar ta Masar.
Jami'i mai kula da manufofin hulɗa da ƙasashen waje a Tarayyar Turai, Josep Borrell shi ma ya tabbatar a ranar Litinin cewa an kwashe ‘yan ƙasashen Turai fiye da 1,000.
Afirka ta Kudu da Kenya da kuma Uganda na cikin ƙasashen Afirka da suka sanar da kwashe mutanensu.
Gwamnatin Burtaniya ta sanar cewa za ta fara kwashe jami'anta da iyalansu na kusa daga ranar Litinin.
A ranar Litinin, Mista Blinken ya bayyana cewa ayarin wasu motoci da ke ƙoƙarin fitar da mutane sun fuskanci ‘’fashi da kwasar ganima’’.
Ya kuma ce Amurka na duba yiwuwar barin ayyukanta na diflomasiyya don ci gaba da aiki a Sudan, amma ya bayyana halin da ake ciki a can da cewa "mai cike da ƙalubale ne".
Ana ci gaba da tserewa
Kasar Sudan ta fuskanci katsewar layukan sadarwar intanet ranar Lahadi, yayin da ake gwabza faɗa, amma tun tuni suna ɗan dawowa jefi-jefi, a cewar wata cibiya mai sa ido ta NetBlocks.
An yi ƙididdigar cewa dubban ɗaruruwan mutane ne da suka hadar da ‘yan ƙasar ta Sudan da waɗanda suka fito daga ƙasashe maƙwabta ne suka tsere saboda tashin hankalin.
Hassan Ibrahim, mai shekara 91 yana cikinsu. Yana kuma zaune ne a kusa da babban filin jirgin saman Khartoum, inda wasu mummunar arangama ta faru, amma tuni ya yi bulaguro mai cike da hatsari tare da iyalansa zuwa ƙasar Masar mai maƙwabta.
Ya shaida wa BBC cewa sun tsere daga faɗawa tarkon rikicin da ake gwabzawa tsakanin mayaƙan RSF da sojojin Sudan amma harin ya ritsa da wata motar a-kori-kura da ke bin su a baya.
Daga nan ne iyalan suka shiga cikin wata motar bas zuwa kan iyaka, tafiyar da ta ɗauke su tsawon sa’a 12, amma sai suka iske dandazon jama’a masu jiran a ba su izinin shiga ƙasar ta Masar.
"Akwai iyalai da dama da suka ƙunshi tsofaffi, da ƙananan yara da jarirai," a cewar Ibrahim. "'Yan Sudan na tsere wa ƙasarsu- abin baƙin ciki!"
Eiman ab Garga, wata likitar mata ‘yar asalin Sudan mazauniyar Burtaniya, na ziyara a birnin Khartoum tare da ‘ya'yanta a lokacin da faɗan ya ɓarke, kuma an kwashe su zuwa ƙasar Djibouti a wani jirgin sama da ƙasar Faransa ta tanada.
Tafiyar gaggawar na nufin ba ta iya yin sallama da mahaifinta maras lafiya, da mahaifiyarta da kuma ‘yar'uwarta ba.
"Ƙasar cike take da datti, akwai tulin shara ko'ina,’’ ta shaida wa BBC. "Akwai dagwalon bahaya da ke ta ɓulɓulowa, yana wari, don haka yanzu muna gab da faɗawa cikin mummunan yanayin ɓarkewar cutuka da rashin lafiya, kuma ba za a samu asibitocin zuwa ba".











