Yaya duka ɓangarorin da ke faɗa a Sudan ke iƙirarin samun nasara?

Sudan Crisis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rarrabuwar kai a tsakanin dakarun sojoji a Sudan shi ne tushen wannan rikici na ƙwace iko

An kasa ganewa ƙarara ko wane ne yake da iko da gwamnati a Sudan.

Bayanai masu cin karo da juna na fitowa, yayin da aka ci gaba da gwabza mummunan faɗa ranar 15 ga watan Afrilu tsakanin sojoji da dakarun kai ɗauki don tallafawa ayyukan tsaro na RSF.

An kashe a ƙalla mutum 83 a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, yayin da rikici ya fantsama daga Khartoum babban birnin ƙasar zuwa sauran birane.

Rashin kafar yaɗa labarai ta gwamnati - wadda kwatsam ta dakatar da shirye-shirye bayan wani artabu a hedkwatarta da ke Omdurman - ya sa rundunar sojojin Sudan da dakarun RSF sun koma amfani da shafukan sada zumunta suna fitar da bayanai masu cin karo da juna.

Bayanan sun haɗar da iƙirarin iko da muhimman wurare kamar cibiyoyin ba da umarni na dakarun soja da sansanonin sojojin sama da kuma fadar shugaban ƙasa.

Rikice-rikicen sun ta'azzara ne saboda gwagwarmayar neman iko tsakanin babban hafsan rundunar soji kuma jagoran Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa da ke iko da dakarun RSF, Janar Hamdan Dagalo wanda aka fi sani da Hemeti.

Tun bayan karkatar da wani juyin-juya-halin fararen hula da ya hamɓarar da Shugaba Omar al-Bashir wanda ya daɗe a kan mulki a 2019, rundunar sojin ƙasar ta tattare iko a hannunta.

Wa za a zarga kan faɗan da ya ɓarke?

Dakarun biyu sun yi ta zargin juna game da ko wanne ɓangare ne ya fara tada rikicin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kwanaki kafin ɓarkewar faɗan, an ba da rahoton cewa rundunar RSF ta yi ta jibge dakaru a Khartoum da kuma muhimmin garin Marawi na arewacin Sudan.

Rundunar sojojin Sudan ta bayyana matakin dakarun RSF a matsayin "haramtacce" kuma "mai cike da hatsari".

A ranar 15 ga watan Afrilu, rundunar RSF ta fitar da wata sanarwa a shafinta na Facebook tana iƙirarin cewa "ɗumbin sojojin ƙasa na Sudan sun kutsa kai cikin sansanonin dakarunta" a Khartoum, inda suka yi musu ƙofar rago.

Sai dai sojoji, sun yi iƙirarin cewa dakarun RSF ne suka yi yunƙurin ƙwace hedkwatocin sojojin ƙasar da ke cikin babban birnin.

Kuma a cikin jerin sanarwar da ta fitar daga bisani, rundunar sojin Sudan ta fara bayyana rundunar RSF a matsayin "'yan tawaye" ko kuma "sojojin sa-kai masu tawaye".

Lamarin dai ya daɗa harzuƙa rundunar jami'an ta masu kayan sarki, wadda batun shigar da dakarunta cikin rundunar sojojin Sudan ya zama sanadin dambarwar siyasar da ta shiga tsakaninsu.

An kafa rundunar masu kayan sarki ta RSF ne a shekara ta 2013.

Mafi yawan dakarunta kuma mayaƙan ƙungiyar sojojin sa-kan nan ne da ta yi ƙaurin suna wato Janjaweed, wadda cike da rashin imani ta murƙushe wani tawaye a lardin Darfur na yammacin Sudan.

Rundunar sojin Sudan ta wallafa bidiyo da dama a shafinta na Facebook ranar 16 ga watan Afrilu.

Bidiyon dai na iƙirarin nuna yadda dakarun sojoji suka yi fata-fata da sansanonin mayaƙan RSF a sassan ƙasar da dama tana cewa "nasara saura ƙiris".

Waɗanne wurare aka aukawa da faɗa?

Sudan Crisis

Asalin hoton, BBC Monitoring

Bayanan hoto, Ana fargabar cewa faɗa tsakanin dakarun Sudan zai iya ta'azzara rikice-rikicen da ke faruwa a ƙasashen yankin

Sansanonin rundunar sojin Sudan da dakarun RSF na nan a wurare da yawa na faɗin ƙasar, abin da ya janyo fafutukar ƙwace cibiyoyin ba da umarni ga dakarun tsaro, lamarin da lokaci zuwa lokaci yake kassara duk wani yunƙuri na haɗa kan sojojin Sudan.

A cewar jaridar intanet ta Sawt al-Hamish mai zaman kanta a ranar 15 ga watan Afrilu, dakarun RSF sun yi iƙirarin ƙwace babbar cibiyar bai wa sojoji umarni da hedkwatocin rundunonin sojoji a jihar Darfur.

Ta kuma yi iƙirarin ƙwace iko da sararin saman Sudan.

Sai dai rundunar sojin Sudan ta musanta hakan, tana cewa Rundunar Sojojin Saman Sudan "za ta gudanar da wani cikakken safiyo na yankunan da dakarun RSF masu tawaye suka yi sansani".

Dakarun RSF masu kayan sarki sun kuma zargi wata ƙasar waje da yin luguden bama-bamai kan wuraren da mayaƙanta suka ja daga a jihar Red Sea da ke gabashin ƙasar.

Sun kuma yi "gargaɗin mummunan sakamako", a cewar tashar talbijin ta Al Jazeera.

Sojoji da dakarun RSF duka sun ba da rahoton gwabza mummunan faɗa don ƙwace filin jirgin saman Khartoum da na Marawi da kuma sansanonin sojojin sama na Al-Obeid.

Tashar Sky News mai sansani a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ba da rahoto a ranar 15 ga watan Afrilu cewa dakarun ƙasar Masar da ke cikin Sudan don ayyukan soja na haɗin gwiwa sun "miƙa kai" ga dakarun RSF a Marawi.

Wani bidiyo ya nuna adadin wasu mutane sanye da kakin sojoji suna dudduƙe tare da yin magana da mayaƙan rundunar RSF cikin karin harshen Larabcin Masar.

Hemeti dai ya faɗa wa tashar Sky News ta Larabci cewa sojojin Masar ɗin suna nan cikin aminci, kuma dakarunsa sun ba su abinci da ruwa, sannan a shirye ya ga yadda za a mayar da gida, tashar ta ce.