Kasashen Yamma sun gargadi sojojin Sudan kan nada Firaminista

Asalin hoton, AFP
Kasashen Birtaniya da Amurka da Norway da kuma Tarayyar Turai sun gargadi sojojin da ke rike da iko a Sudan a kan nada Firaminista nasu da cewa muddin suka yi hakan akwai hadarin su jefa kasar ta gabashin Afirka cikin Karin rikici.
Kasashen sun ce ba za su bayar da goyon baya ga Firaminista ko gwamnatin da sojojin za su nada b aba tare da sa hannun masu ruwa da tsaki na farar hula ba.
Tsohon Firaministan kasar Abdalla Hamdok, ya sauka daga mukaminsa ne a ranar Lahadi yayin da kasar ke fama da rikicin siyasa da kuma zanga-zanga da ake ta yi a fadin kasar saboda juyin mulkin da soji suka yi a watan Oktoba.
Kasashen na yammacin duniya sun kuma kara yin gargadi a kan irin matakin da sojojin Sudan din ke dauka a kan masu zanga-zanga, inda aka kashae mutane sama da hamsin a cikin masu zanga-zangar tun bayan juyin mulkin.

Asalin hoton, AFP
Wani mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya Stéphane Dujarric, ya ce majalisar na lura da abubuwan da ke wakana da kyau, tare da kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki a rikicin da su ci gaba da tattaunawa a kan makomar kasar ta Sudan:
Ya ce, "Babban Sakatare na karfafa guiwar dukkanin masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tattaunawa mai ma'ana domin cimma mafita da ta kunshi kowa da kowa, da zaman lafiya kuma mai dorewa.
Fatan 'yan Sudan na samun cikakken mataakin da zai kai ga mayar da kasar kan mulkin dumokuradiyya na da muhimmanci . Ba shakka a tsaye muke kyam mu ci gaba da goyon bayan wannan kokari, a nan da kuma ta hanyar wakilinmu na musamman Volker Perthes da ke can."
Ko a jiya Talata jami'an tsaro sun rika amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa dubban masu zanga-zangar kin jinin mulkin sojin.











