Dalilin da ya sa rikicin Sudan ya ki ci ya ki cinyewa

Asalin hoton, AFP
Jami'an tsaro a Sudan sun harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zanga a Khartoum, babban birnin kasar inda suke neman a mika mulki hannun farar hula.
Daruruwan jama'a ne suka taru kusa da fadar shugaban kasa a gangamin da suke gudarwa kowane mako.
Masu zanga-zangar na nuna adawa da hambarar da mulkin farar hula da sojoji suka yi cikin watan Oktoba.
Sun kuma soki yarjejeniyar da aka cimma wadda ta ba da ikon mayar da Firaminista Abdalla Hamdok kan mukaminsa.
Janar Abdel Fattah al-Burhan ya rusa majalisar mulkin soja da farar hula a ranar 25 ga watan Oktoba da aka kafa domin jagorantar kasar kan tafarkin dimokuradiyya tare da ayyana dokar ta baci a fadin kasar.
Zanga-zangar gama-gari da kuma yin Allah wadai da matakin nasa ya tilastawa al-Burhan, wanda shi ne shugaban majalisar gudanarwa, mayar da Hamdok kan mukaminsa a watan jiya. Ya kuma yi alkawarin gudanar da zabe a watan Yulin 2023 tare da mika mulki ga zababbiyar gwamnatin farar hula.
Sai dai kungiyoyin da ke fafutukar tabbatar da dimokuradiyya, wadanda ke kan gaba a zanga-zangar da ta hambarar da al-Bashir, sun soki yarjejeniyar maido da Hamdok. Sun ce bai kamata sojoji su kasance cikin gwamnati ba saboda ba za a amince da su su jagoranci tafiyar da mulkin dimokradiyya ba.
Sai dai wasu masana na ganin ya kamata masu zanga zangar su yi hakuri , su jira har zuwa lokacin da sojoji su ka yi alkawarin cewa za su mika mulki ga farar hula.
Sun ce rashin hakuri ne ya sa kawo yanzu zanga zangar ta ki ci ta ki cinyewa kamar yadda Ambassada Sulaiman Dahiru, tsohon jakadan Najeriya a Sudan ya shaidawa BBC.
" Rashin hakuri ne ya yi mu su yawa saboda an riga an kawarda gwamnatin Albashir kuma tun da sojoji sun ce 2023 ne za su mika wa farar hula mulki,toh ni a gani nay a kamata mutane su yi hakuri" in ji shi.
A cewar masanin rashin hakuri ba zai biya mu su bukata ba,sai dai ya ce akwai rashin aminci tsakanin masu zanga-zangar da sojojin kasar.
"Suna ganin wadanan sojojin su ma ba za su sauka daga kan mulki ba, za su yi irin na Albashir ne".
Bayan juyin mulkin na ranar 25 ga watan Oktoba, zanga-zangar da ta gabata ta ci karo da wani kazamin harin da ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 50 tare da jikkata daruruwa, akasari ta hanyar harbin bindiga, a cewar kungiyar likitocin masu rajin kare demokradiyya.
Al-Burhan ya dage kan cewa kwace mulkin da sojoji suka yi ba juyin mulki ba ne, amma mataki ne na "gyara mika mulki" zuwa ga cikakken dimokuradiyya wanda ya fara da hambarar da al-Bashir a 2019.











