Sudan: Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga a Khartoum

Asalin hoton, AFP
Jami'an tsaron Sudan sun yi ta harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zanga da suka mamaye titunan babban birnin kasar Khartoum.
Haka kuma, jami'an tsaron sun tsare malaman makaranta da suka shiga zanga-zangar.
Da tsakar dare masu boren sun kafa shingaye a ranar farko ta zanga-zangar kwanaki biyu da aka shirya yi ta adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi a watan da ya gabata.
Bukatarsu dai ita ce, gwamnatin soji da matsa gefe tare da mayar da mulki hannun farar hula.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da masu shiga tsakani na kungiyar kasashen Larabawa suka isa
Khartoum domin tattaunawa dan magance matsalolin.
Har yanzu Firai Minista, Abdalla Hamdok, na hannun sojoji karkashin daurin talala, kuma sojojin na matsa masa lambar ba su hadin kai ta kowace fuska, kamar yadda wakilin BBC Andrew Harding ya rawaito daga birnin Khartoum.
A watan da ya gabata ne jagoran juyin mulkin, Janaral Abdel Fattah al-Burhan, ya wargaza gwamnatin farar hula, tare da kame shugabannin 'yan siyasa da ayyana dokar ta-baci a kasar.
Rashin hanyar sadarwar intanet na kwanaki biyu, ya janyo mutane ba su san abin da ke faruwa ba, sai dai bayan kwanakin nan malaman makaranta sun yunkuro tare da fara zanga-zangar kin amincewa da juyin mulkin, inda suka yi na su boren a kusa da ma'aikatar ilimi.
Wani malamin makaranta mai suna Muhammad Al-Amin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa; ''Mun shirya zanga-zangar lumana domin kin amincewa da abin da Burhan ya yi a gaban ma'aikatar limi, amma daga bisani 'yan sanda suka zo tare da jefa mana hayaki mai sa hawaye, saboda kawai muna adawa da abin da ke lalata ma na kasa."
A arewacin birnin Khartoum, jami'an tsaro ne ke sintiri rike da hayaki mai sa hawaye da gurneti a hannunsu, cikin shirin ba sani ba sabo, in ji kamfanin dillancin labarai na Reuters.
'Sojoji ba za su mulke mu ba'
Har yanzu wadanda sojoji suka lakada wa duka, wasu har da harbin bindiga na kwance a wani asibitin kudi mai suna Royal Care a birnin Khartoum inda ake musu magani.
Cikinsu akwai matashin dalibi Faisal mai shekara 18, wanda aka harba har sau biyu a kafarsa a lokacin zanga-zanga ta baya-bayan nan.
"An harbe ni tare da wasu mutum 9, ba su wani gargade mu ba kafin harbin, kawai sun bude mana wuta ne. sojojin nan, hmmm kamar dabbobi suke, kai watakila ma dabobi sun fi su," in ji dalibin.
A yanzu an yi masa tiyata har sau uku a kafarsa ta dama, ya kuma kara nanata cewa babu gudu ba ja da baya kan aniyarsu ta adawa da mulkin soji, kuma wannan bai karya musu gwiwa ba. "Manufarmu ba ta sauya ba, ba mu tsorata ba, ba za mu amince sojoji su mulke mu ba."
A daya gadon da ke kusa da Faisal, wani tsohon tela ne mai shekara 54, sunansa Yasir Muhammad Ali Abdulla, 'yan uwansa sun kewaye shi.
Shi ma ya rufe shagonsa tare da shiga zanga-zangar a washegarin da aka yi juyin mulkin.
Ya ce da "gangan wasu sojoji suka bi ta kan masu zanga-zangar a kusa da filin jirgin sama na birnin Khartoum.
Bayan haka, sojoji shida suka lakada min duka da sanda a bayana da kirjina, saboda kawai muna bukatar 'yancinmu. Idan har sojoji ba za su iya kare mu ba, ba za su yi mana adalci ba, su cire kakin soji su bari farar hula su yi mana abin da muke so."











