Juyin mulkin Sudan: Abin da ya sa sojoji suke wasa da makomar kasar

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Daga Alex de Waal
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa analyst
Mutumin da ya jagoranci juyin mulki a Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan ya yi gurguwar dabara.
Ya sanya wa kasashen duniya shakku kan Sudan a matsayinta na jaririyar kasar da ta karbi mulkin dimokuradiyya, ya kuma sa za ta fuskanci matsala wajen biyan bashin da kasashen duniya suke bin ta da ma irin tallafin da ake ba ta, kana ya jefa shirin zaman lafiya da ake yi da 'yan tawayen Darfur da Nuba Mountains cikin garari.
Shi ne shugaban Majalisar Koli ta Sudan kuma wanda ke wakiltar sojoji a gwamnatin hadakar da suka yi da farar hula - gabanin ranar Litinin, lokacin da ya kwace iko baki daya.
Ya rusa majalisar zartarwar farar hula, ya kama Firaiminista Abdalla Hamdok da wasu manyan shugabannin farar hula wadanda sojoji suka amince su raba daunin iko da su zuwa lokacin da za a gudanar da zabe a shekara mai zuwa.
Bukatar janar din ta mulkin kama-karya ta wani boyayyen abu ba ne.
A cikin watannin da suka gabata, ya nuna kosawa da mulkin Mr Hamdok, yana nuna cewa akwai bukatar samun shugaba mai karfi domin ceto kasar.
A wani gangami da aka gudanar kwanakin baya domin nuna goyon baya ga sojoji a Khartoum, masu zanga-zangar sun zargi Mr Hamdok bisa tabarbarewar lamura - bai taimaka wajen warware cunkoso a tasoshin jiragen ruwa ba lamarin da ya haifar da karancin abubuwan more rayuwa.
Masu fafutikar mulkin dimokuradiyyar Sudan sun kadu da ganin irin tsare-tsaren sojoji, wani abu da suke ganin sun koya daga Abdul Fatah al-Sisi lokacin da yake shirin kwace ikon gwamnatin Masar a 2013.
Kungiyar Kwararru ta Sudan da kuma kungiyoyi da dama da suka shiga zanga-zangar lumana da ta kawo karshen mulkin shekaru 30 na Shugaba Omar al-Bashir a 2019 sun shirya gudanar da jerin zanga-zanga.

Asalin hoton, EPA
Jakadun kasashen wajen sun nuna damuwarsu. Manzo na musamman na Amurka Jeffrey Feldman ya kai ziyara Khartoum a karshen mako domin ganin tattaunawa tsakanin janar-janar da farar hula ta dore. Ya bar birnin ranar Lahadi inda ya yi tunanin cewa sun amince su ci gaba da aiki tare.
An gudanar da juyin mulkin ne awanni kadan bayan ya bar kasar, lamarin da ya yi matukar bata ran Amurka.
Amurka ta bayyana karara cewa an yaudare ta, lamarin da ya sa ta "dakatar" da $700m (£508m) na tallafin da take bai wa kasar.
Wata babbar matsala ita ce matsayin bashin Sudan, wanda a kwanakin baya Mr Hamdok ya tattauna kan yadda za a rage shi.
Bayan shekaru biyu ana jinkiri, ana sa ran samun tallafi daga kasashen duniya domin farfado da tattalin arzikin Sudan -amma yanzu babu tabbaci kan hakan.
Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Gabashin Afirka da dukkan kasashen Yamma da ke tallafa wa Sudan sun yi tur da juyin mulkin sannan suka yi kira a koma turbar dimokuradiyya.
Ita ma kungiyar kasashen Larabawa ta yi kira a mutunta tsarin mulki. Galibi kungiyar tana dasawa da gwamnatin Masar, abin da ya sa ake tambaya kan irin taimakon da Janar Burhan zai iya samu daga Alkahira.
Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, wadanda suka bayar da tallafin kudi ga Janar Burhan a 2019, ba su ce komai ba kawo yanzu.
Watakila suna goyon bayan sojoji, sai dai a sane suke cewa ba za su iya biyan kudin ceto Sudan daga kangin da take ciki ba.
Da ma dai Janar Burhan shi ne mafi karfin fada a ji a kasar, inda ya samu goyon bayan bangarorin da suka kulla yarjejeniyar kafa gwamnatin hadaka a watan Agustan 2019.
Don haka me ya sa ya yi watsi da wannan dama domin kwace mulki?
Zarge-zargen cin hanci
A tsarin yarjejeniyar, a watan gobe ya kamata Janar Burhan ya sauka daga mukamin shugaban Majalisar Koli.
Daga nan kuma farar hular da aka zaba zai zama shugaban kasa, sannan fararen hular da ke cikin gwamnati za su fi samun damar aiwatar da manyan kudurorin gwamnati.
Daya daga cikinsu shi ne bin kadi game da take hakkin dan adam. Gwamnati ta amince ta mika tsohon shugaban kasar ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya.
Tsofaffin mataimakansa - wadanda suka hada da Janar Burhan da kuma shugaban runduna ta musamman ta masu sanye da kayan sarki Janar Mohamed Hamdan "Hemeti" Dagolo - sun fi so a yi masa shari'a a Sudan ba a The Hague ba.
Suna da kwakkwaran dalili da ya sa suke son hakan domin kuwa zai iya sanya sunayensu a cikin wadanda suke da hannu a ta'asar da aka yi a yakin Darfur.

Janar Burhan da sauran abokansa sojoji suna da karin dalilai na yin fargabar cewa idan aka gudanar da bincike kan kashe-kashen da suka faru a Khartoum a watan Yunin 2019 za a iya dora musu alhakin abubuwan da suka faru.
Lamarin ya faru ne watanni biyu bayan sojoji sun hambarar da Bashir, lokacin da masu zanga-zangar lumana suke kira a koma kan mulkin farar hula.
Magance matsalar cin hanci da kuma yin garanbawul kan fannin tsaro na cikin abubuwan da suke damun janar-janar din.
Mr Hamdok ya shahara wajen sukar sojoji bisa tsoma hannu cikin harkokin tattalin arziki.
Sojoji suna cinye babban kaso na kasafin kudin kasar sannan suna da kamfanonin da ba sa biyan haraji, wadanda ake zargi da cin hanci a tsarin bayar da kwangilarsu.

Asalin hoton, AFP












