Abdalla Hamdok: Firaministan Sudan ya ajiye mukaminsa

Asalin hoton, Reuters
Firaministan Sudan Abdalla Hamdok ya sauka daga mukaminsa, yayin da kasar ke fama da dambarwar siyasa bayan juyin mulkin soji da ya haifar da cikas ga kokarin kasar na komawa mulkin dumokuradiyya.
Mista Hamdok yana daga cikin tsarin da aka yi a raba ikon gwamnati tsakanin sojoji da farar hula, wadanda suka jagoranci boren hambarar da dadadden tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir, a watan Afrilu na 2019.
Saukar tasa ta zo ne bayan wata ranar da aka kara shafewa a na gagarumar zanga-zanga wadda jami'an tsaro suka kashe akalla mutane biyu.
Kungiyar likitoci ta Sudan din wadda ke daga cikin kungiyoyin da ke fafutukar tabbatar da dumokuradiyyar a ranar lahadi, ta ce daya daga cikin mutanen da aka kashe an doke shi ne ga kai, yayin da yake cikin masu zanga-zanga a Khartoum
Mutum na biyun kuwa kungiyar ta ce an harbe shi ne a kirji a birnin Omdurman, inda ta kara bayani da cewa akwai gwamman masu zanga-zangar da jami'an tsaro suka raunata.

Asalin hoton, AFP
A jawabin da ya yi na sauka daga mukamin wanda aka yada ta talabijin ranar Lahadi da daddare, Hamdok wanda ya kulla yarjejeniya da sojoji a watan Nuwamba bayan da suka cire shi a watan Oktoba tare da yi masa daurin talala a gida kafin su dawo da shi bayan wata daya, ya ce akwai bukatar a yi wata tattaunawa domin cimma wata sabuwar yarjejeniya ta mayar da kasar kan turbar dumokuradiyya.
Dubban jama'a ne a Khartou babban birnin kasar da sauran birane suke ci gaba da zanga-zanga, inda 'yan kasar ke son ganin dole sai an samar da cikakkiyar gwamnatin farar hula.

Asalin hoton, AFP
A ranar Lahadi jami'an tsaro suka rika harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zanga inda suka kashe mutane da dama, ko da yake jami'ai ba su ce komai ba game da kisan.
Akalla mutane 56 aka hallaka tun da aka fara zanga-zangar kin yarda da juyin mulkin da soji suka yi ranar 25 ga watan Oktoba 2021.
Jagoran juyin mulkin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya kare juyin mulkin na watan Oktoba, yana cewa sojojin kasar sun yi shi ne domin kare kasar daga fadawa yakin basasa wanda ke barazanar barkewa.
Janar din ya ce har yanzu Sudan na kan hanyar komawa ga mulkin farar hula inda aka tsara gudanar da zabe a watan Yuli na 2023.











