Juyin mulkin Sudan: Bayanai dalla-dalla kan yadda komai ya wakana

Asalin hoton, AFP
Juyin mulkin da ya faru a Sudan, inda yanzu haka firaminista da ministoci ke garƙame bayan rusa gwamnati, ya kasance rikici na baya-bayanan da ake gani ko ke girgiza kasar.
Baya ga tashin hankalin rikicin siyasa, tattalin arzikin Sudan ya faɗa cikin ruɗani, ana fuskantar hauhawar farashi da karancin abinci da man fetur da magunguna.
Juyin mulkin ya ɗaga hankulan manyan ƙasashen duniya wanda a kwanan baya-bayan nan suka soma dawo da alaƙarsu da Sudan bayan tsawon shekaru na ƙaurace mata.
Ga abubuwan da ya kamata ku sani.
Me ya jawo juyin-mulkin?
Shugabannin sojoji da farar-hula ke iko a kasar tun Agustan 2019 bayan hamɓarar da gwamnatin shugaba mafi daɗewa a karagar mulkin ƙasar, Omar al-Bashir.
Sojoji suka hamɓarar da Bashir, sai dai zanga-zangar jama'ar gari kan buƙatar mulki ya koma hannun farar-hula sun tilastawa sojoji yin maslaha da zummar mayar da mulki kan turbar dimokuraɗiya.
Yanzu kamata ya yi a ce ƙasar na ƙarƙashin gwamnatin riƙon-kwarya, inda farar-hula da sojoji za su jagoranci ƙasar tare ƙarkashin kwaminitin haɗin-gwiwar da aka kafa.
Amma sai ya kasance ɓangarorin biyu sun fuskanci rashin jituwa.

Me ya haddasa tashin hankalin?
Shugabannin sojoji a gwamnatin riƙon-kwarya sun buƙaci sauye-sauye daga abokan huldarsu farar-hula da neman sauya majalisa. Sai dai shugabannin farar-hula da ke rigimar mulki sun yi watsi da wannan bukatar.
Tun 2019 ake kokarin hamɓarar da gwamnatin wanda bai yi nasara ba, na baya-bayan nan shi ne wanda aka gani a watan da ya gabata.
Babban jagorar farar-hula, Firaminista Abdallah Hamdok, ya zargi masu biyayya ga Bashir - wanda akasarin su ake cewa suna cikin sojoji, hukumomin tsaro da cibiyoyin gwamnati.
A makonnin baya-bayan nan an fuskanci zanga-zanga daga masu goyon bayan sojoji a birnin Khartoum, da kuma wasu dandazon jama'a da suka fito domin nuna na su goyon-bayan ga firaministan kasar.
Masu zanga-zangar goyon-bayan sojoji sun zargi gwamnati da nuna gazawa wajen sake farfaɗo da ƙasar.
Kokarin Mista Hamdok na sake farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar - ciki har da zaftare tallafin man fetur - bai samu gamsuwar mutane ba.
Rikicin siyasar Sudan abu ne da ya jima yana kasara ƙasar.
A shekarun baya rabuwar kawuna tsakanin jam'iyyun siyasa da gazawa wajen haɗa-kai sun buɗe kofa da bai wa sojoji damar shiga harkar siyasar ƙasar, da aiwatar da juyin-mulki da sunan kokarin dawo da ƙasar kan turba a cewar mai shari Magdi Abdelhadi.
A yau Sudan, akwai akalla jam'iyyun siyasa 80.
Irin wannan rabuwar kawuna da ɓangaranci su suka taka rawa a gwamnatin riƙon-ƙwarya, abin da ya kai ga samun rabuwa tsakanin sojoji da farar-hula har aka kai ga matsayin da ake ciki yanzu.

Me ke faruwa a yanzu?
Jagoran sojojin da suka yi juyin mulki ya gabatar da jawabi da ke ayyana dokar ta baci da rusa majalisar ministoci da gwamnoni.
Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan ya ce za kuma a gudanar da zaɓuka a watan Yulin 2023.
Rahotanni na cewa an garƙame firaminista Hamdok bayan hamɓarar da shi, da wasu ministocinsa. Sannan sojoji sun karɓe ragamar tashoshin talabijin da rediyo na ƙasar.
An kuma katse layukan intanet.
Ƙungiyar haɗin-kan Afirka, AU da Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai da Ƙungiyar ƙasashen labarawa da Amurka sun yi alla-wadai da juyin-mulkin Sudan.

Me zai iya faruwa nan gaba?
Juyin mulkin ba lallai ya kasance karshen rikicin ƙasar ba, a cewar mai sharhi kan ƙasashen Afirka Alex de Waal, kalmomin da ke kasancewa kamar "ƙarfafa gwiwa ga farar-hula".
Duk lokacin da sojoji suka yi irin wannan yunkuri "mutane na fantsama kan tittuna da ƙoƙarin daƙile su - kuma ina da yaƙinin cewa tarihi na iya sake maimaita kansa a wannan karon", ya shaidawa BBC Newshour.
A cewar wasu bayanai da ma'aikatar labarai ta wallafa a shafin Facebook, firaministan ya yi kira ga 'yan ƙasar su fito su marawa gwamnatinsa baya.
Hotuna da rahotanni da ke fitowa daga Khartoum na nuna yadda masu zanga-zanga suka fantsama akan manyan tittunan birnin.
An tura sojoji kowanne yanki domin taƙaita zirga-zirga.
A watan Yunin 2019, kafin cimma daidaito da kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya, sojoji sun buɗe wuta kan masu zanga-zanga a Khartoum da kashe mutum 87.
Jimamin wannan rana abu ne da wadanda abin ya faru kan idansu ba za su taɓa mantawa ba.












