Janar-janar ɗin da ke rikici don mallakar Sudan

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Janar Mohamed Hamdan Dagalo (a hagu) da Janar Abdel Fattah al-Burhan (a dama)

Ƙarar tashin bama-bamai, da turnuƙewar baƙin hayaƙi a sararin samaniya, da fargaba a kullum da zaman rashin tabbas a yayin da ruwan harsasai da makaman roka da kuma jita-jita ke bazuwa.

Rayuwa a Khartoum babban birnin Sudan da sauran sassan ƙasar da dama ta ƙara taɓarɓarewa fiye da kima.

A tsakiyar wannan dambarwa, akwai janar-janar ɗin soja biyu: Abdel Fattah al-Burhan, shugaban rundunar sojin ƙasar (SAF) kuma jagoran Sudan (SAF), da Mohamed Hamdan Dagalo, da aka fi sani da Hemedti, jagoran dakarun kai ɗaukin gaggawa don tallafawa ayyukan tsaro (RSF).

Duka biyun sun yi aiki tare, sannan a tare suna gudanar da wata gwamnati da aka kafa bayan wani juyin mulki – yanzu gwagwarmayar ƙwace iko a tsakaninsu na yin kaca-kaca da Sudan.

Dangantakar mutanen biyu ta jima da wanzuwa.

Dukanninsu sun taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da ayyukan ta-da-ƙayar baya a kan ‘yan tawayen Darfur, yankin yammacin Sudan da ya fama da yaƙin basasa tun daga shekarar 2003.

Janar Burhan ya samu ƙarin girman riƙe ikon rundunar sojin Sudan a yankin na Darfur.

Hemedti shi ne kwamandan ɗaya daga cikin ƙungiyoyin Larabawa masu rike da makamai da dama, waɗanda gaba ɗaya ake kiran su da suna Janjaweed, wadda gwamnati ta kafa don murƙushe ƙungiyoyin ‘yan tawaye da ba na Larabawa ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

The military has been running Sudan for most of its post-independence

Majak D'Agoot shi ne mataimakin daraktan harkokin leƙen asiri da ayyukan tsaron ƙasa a wancan lokacin – kafin ya zama muƙaddashin ministan tsaro a Sudan ta Kudu lokacin da ta ɓalle a 2011.

Ya gamu da Janar Burhan da Hemedti a Darfur, kuma ya ce sun yi aiki sosai tare.

Amma ya shaida wa BBC cewa ya ga 'yar alama cewa kowanne daga cikinsu zai gawurta ya kai wani matsayi mafi girma a ƙasar.

Hemedti dai jagoran sojojin sa-kai ne "da ke taka rawa wajen yaƙi da 'yan ta-da- ƙayar-baya, da taimaka wa rundunar sojoji", shi kuwa Janar Burhan ƙwararren soja ne, duk da yake "da duk burin wani jami’in sojin Sudan, komai zai iya faruwa".

Sojoji sun daɗe suna gudanar da harkokin mulki a Sudan bayan tsawon lokacin da ta samu ‘yancin kai.

Dabarun gwamnati a yankin Darfur, da wani ƙwararre ɗan Sudan Alex de Waal ya bayyana da "yaƙi da ayyukan tayar da ƙayar baya cikin sauki", ya yi amfani da dakarun ƙasar, da ƙabilu masu gwagwarmaya da makamai da ƙarfin soji ta sama wajen yaƙar ‘yan tawaye – ba tare da kula da tsaron rayukan fararen hula ba.

An bayyana yankin na Darfur a matsayin yankin kisan kare dangi na farko a ƙarni na 21, inda aka zargi mayaƙan Janjaweed da aikata kisan kare dangi da amfani da fyaɗe a matsayin makamin yaƙi.

Daga ƙarshe Hemedti ya zama kwamandan abin da za a iya bayyanawa da wani gyauron ƙungiyar mayaƙan Janjaweed, ta hanyar rundunarsa ta RSF.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An zargi mayakan Janjaweed da aikata kisan kare dangi da aikata fyade a lokacin rikicin Darfur

Ƙarfin ikon Hemedti ya yi matuƙar ƙaruwa lokacin da ya fara samar da dakarun da za su fafata a yaƙin da rubdugun dakarun da Saudiyya ke jagoranra a Yemen.

Jagoran rundunar sojin Sudan, Omar al-Bashir, ya dawo yana dogara da Hemedti da mayaƙan ƙungiyar RSF a matsayin wani ƙarin ƙarfi a kan dakarun sojin da ake da su, cike da fatan zai kasance da matukar wahala ga wasu ɗaiɗaikun ƙungiyoyin masu riƙe da makamai su hambarar da shi daga mulki.

Daga ƙarshe – bayan shafe wata guda ana zanga-zangar da ta samu karɓuwa – janar-janar ɗin sun haɗa kai inda suka hambarar da Bashir, a watan Afrilun 2019.

Gaba kaɗan cikin shekarar, sai suka rattaba hannu kan yarjejeniya da masu zanga -zangar ta kafa gwamnati da fararen hula ke jagoranta da haɗin gwiwar rundunar soji wadda Janar Burhan ke shugabanta, Hemedti kuma matsayin mataimakinsa.

Bayan tsawon shekara biyu – zuwa watan Oktoban 2021 – sai sojoji suka yi juyin mulki, inda har ila yau Janar Burhan ya zama shugaban ƙasa, sannan Hemedti ya sake zama mataimakinsa.

Siddig Tower Kafi mamba ne a majalisar miƙa mulki hannun farar hula a Sudan, don haka yana yawan ganawa da janar-janar ɗin biyu.

Ya bayyana cewa bai ga wata alama da wani ka-ce -na-ce ba, sai bayan juyin mulkin 2021.

Daga nan ne "Janar Burhan ya fara dawo da mambobin ƙungiyoyi masu kaifin kishin Islama da jami’an tsohuwar gwamnati zuwa kan tsofaffin muƙamansu, ya shaida wa BBC.

"Ya nuna karara cewa shirin Janar Burhan shi ne ya dawo da tsohuwar gwamnatin Omar al-Bashir kan mulki."

Mr Siddig ya kuma ce wannan shi ne lokacin da Hemedti ya fara nuna shakku, a yayin da ya fahimici na hannun daman Bashir ba su taɓa nuna masa cikakkiyar yarda ba.

Fitattun mutane daga ƙabilu daban-daban da ke zaune a birnin Khartoum na Kogin Nilu ne a ko da yaushe ke kankane siyasar Sudan.

Hemedti ya fito ne daga yankin Darfur, kuma fitattun mutanen Sudan na yawan magana a kansa da sojojinsa a cikin wasu kalamai na rashin amincewa, a matsayin wanda bai cancanci mulkin ƙasa ba.

A cikin shekara biyu da ta wuce, ya yi ƙoƙarin sa kansa cikin fitattun ‘yan ƙasa, a cikin wakilan tsirarun mutanen da aka ware – tare da ƙoƙarin haɗa ƙawance da ƙungiyoyin ‘yan tawaye a Darfur da South Kordofan da a baya aka umarce shi ya yi kaca-kaca da su.

Ya kuma sha yin magana a kan bukatar da ke da akwai ta dimokradiyya duk da cewa dakarunsa sun ci zali tare da cin zarafin fararen hula masu zanga-zanga a baya.

Rikici tsakanin sojoji da mayakan RSF ya ƙara ta’azzara a yayin da wa’adin kafa sabuwar gwamnati ke gabatowa, tare da mayar da hankali kan batutuwa masu zafi game da yadda za a shigar da dakarun RSF cikin rundunar sojin Sudan.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana iya ganin wuta da hayaki na tashi sama a birnin Khartoum a yayin da dakarun janar-janar din biyu ke arangama

Daga nan ne faɗa ya fara, tsakanin dakarun RSF da kuma rundunar sojojin Sudan, faɗa tsakanin Hemedti da Janar Burhan, na gwagwarmayar ƙwace iko da Sudan.

Ta wani gefen, a ƙalla za a iya cewa Hemedti ya bi sahun manyan ƙusoshin rundunar sojin Sudan, waɗanda yanzu yake yaƙa - a 'yan shekarun da suka gabata, ya kafa wata daular kasuwanci ciki har da a ɓangaren haƙar zinare da sauran manyan harkoki.

Janar Burhan da Hemedti dukkansu na fuskantar kiraye-kiraye daga shugabannin al'umma da mutanen da rikicin Darfur ya shafa, da wasu wuraren daban na gurfanar da su gaban shari’a bisa zargin aikata cin zarafi.

Matsin lambar ya tsananta, sannan akwai dalilai da dama kan yadda waɗannan tsofaffin aminai suka rikiɗe suka zama abokan gabar da ba a ga maciji da juna, waɗanda ba za su ja baya ba.

.