Kasashen Afirka Ta Yamma sun shirya yakar ta'addanci

Asalin hoton, Twitter/Laurestar
Shugabannin kasashen Afirka Ta Yamma sun amince da kashe dala biliyan daya wajen yaki da ta'addanci da ke addabar yankin.
Sun yi wannan alkawarin ne a wani taron Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka Ta Yamma da aka gudanar kan yaki da ta'addanci a Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso a ranar Asabar.
Za a yi amfani da wadannan kudaden domin tallafa wa wannan shiri na musamman na yaki da ta'addanci.
Kamar yadda aka bayyana, wa'adin wannan shirin zai fara ne daga 2020 zuwa 2024. Kudaden za a kashe su wajen kara inganta sojojin da suke yaki da ta'addanci a yankunan da 'yan tada kayar baya suka zama karfen kafa.
A wajen taron, Shugaban Burkina Faso, Roch Marc Christian Kaboré, ya bayyana cewa sakamakon irin barazanar da 'yan ta'adda ke yi a kasashen Afirka Ta Yamma, yana da muhimmanci kasashen su hada kai wajen yaki da ta'addanci.
Ya ce ''a wannan dalili ne ya sa dole ne kasashen su yi amfani da karfinsu da dukiyoyi da kuma tunanisu wajen horar da jami'an tsaro da kuma samar masu da makamai domin yaki da ta'addanci.''

Asalin hoton, Twitter/Laurestar
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da shawara ga shugabanin kasashen yankin kan cewa kada su kuskura su bari 'yan ta'adda su tarwatsa yankin.
Shugaban ya ce ''Yankin mu ya samu ci gaba matuka, kada mu bari 'yan ta'adda su zo su watsa mana yanki, su sa mutanenmu su cire rai daga tsaro da kuma ni'imomin da muke da su.''

Asalin hoton, Twitter/Laurestar
Shugaban hukumar gudanarwa ta Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka Ta yamma Jean-Claude Kassi Brou, ya bayyana cewa irin wannan muhimmin taron, alama ce da ke nuna cewa za a samu hadin kai tsakanin kasashen domin yaki da matsalar da ke damun yankin.
Shi ma Shugaban Jamhuriyyar Niger Mahamadou Issoufou, wanda shi ma yana cikin masu ruwa da tsaki na kungiyar ya bayyana cewa sun kira wannan taron ne sakamakon akwai barazana ga tsaro da tattalin arzikin yankin.
A watan Yulin bana ne Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ana samun kara yaduwar masu yaki da sunan jihadi a Afirka ta Yamma, dole ne a kara kaimi wajen yaki da su.











