Abin da ya sa Afirka ta yamma ke bukatar kudin bai daya

A woman withdraws money at an Orange Money cashier booth

Asalin hoton, AFP

    • Marubuci, Daga Louise Dewast
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Dakar

Kasashe 15 ne a yammacin Afirka suka amince domin amfani da kudin bai-daya da aka yi wa lakabi da ''eco.''

Sai dai kan masana ya rabu dangane da tasirin da wannan kudi na bai daya zai yi ga tattalin arzikin wannan yankin, musamman a kasashen da ke amfani da samfarin kudin CFR franc wadanda kasashe ne na rainon Faransa.

An shafe kusan shekaru 30 ana ta kokarin ganin cewa an cimma wannan buri na amfani da kudin na bai daya.

Sai dai Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato Ecowas, ta bayyana cewa ba za ayi garaje wajen fara amfani da kudin na bai daya ba, a hankali za a fara kuma a kasashen da suka cike sharuddan da aka gindaya za su fara amfani da kudin.

An dai bayar da wa'adin cike sharuddan ne har zuwa shekarar 2020.

Me ya sa Afrika ta yamma ke bukatar kudin bai daya?

Tuni dama kasashe takwas suke amfani da samfarin kudin CFA franc da goyon bayan kasar Faransa.

An bayyana sabon samfarin kudin da aka fitar na bai daya wato eco zai taimaka wa 'yan yankin Afirka ta yamma kusan mutum miliyan 385 domin yin kasuwanci cikin sauki da kuma kara habaka tattalin arzikin kasashen yankin.

Sai dai an koka da cewa Najeriya ita ce ta fi girma da kuma yawan mutane a cikin kasashen kuma ana hasashen cewa za ta mamaye tsare-tsaren tafiyar da kudaden yankin.

Map
Bayanan hoto, Kasashen da ke amfani da samfarin kudin CFA franc
Presentational white space
Presentational grey line

Game da kudin ECO

  • Za a kaddamar da kudin a 2020
  • Kasashe 15 ne na yammacin Afirka za su yi amfani da kudin
  • Farashin musayan kudin zai iya sauyawa tsakanin kasa da kasa
Presentational grey line

Hakan zai faru a 2020?

Ana ganin cewa da kamar wuya duka kasashe 15 na yammacin Afirka su shirya kafin shekara mai zuwa har kuma su fara amfani da kudin.

An yi niyyar kaddamar da kudin bai daya tun a 2003 amma aka yi ta jan kafa ana daga lokaci har 2005 aka zo aka yi niyyar kaddamarwa a 2005 hakan ma bai yiwu ba sai kuma 2010 da kuma 2014 amma kuma a bana Allah yayi an kaddamar.

Zai iya yiwuwa wasu kasashen su cike sharuddan fara amfani da kudin kafin 2020, amma abin tsoron shi ne ko da wasu kasashen sun cike sharudan, shekara ta gaba zai iya yiwuwa wata matsala ta bijiro.

A 2016, kasar Liberia ce kawai ta cike duka sharudda shida da ake bukatar cikewa, babu wata kasa banda Liberiar da cike ko da kuwa sharadi daya.

Wani masanin tattalin arziki Martial Belinga ya bayyana cewa shekarar 2020 shekara ce da ke allamta cewa za a samu nasara.

Ya ce bayar da wa'adi ga kasashe zai taimaka wajen su cike sharuddan da ake bukata.

Anya Najeriya ba za ta mamaye wannan tsarin ba?

Najeriya kasa ce dai da ke takama da arzikin man fetur, masana da dama na ganin za ta mamaye tattalin arzikin yankin muddun aka game kudaden yankin zuwa na bai daya kuma kasashen suka fara amfani da kudin a tsakaninsu.

An misalta hakan ne kuwa da kasar Jamus, kamar yadda ta mamaye tattalin arzikin yankin Turai masu amfani da kudi samfarin Euro, amma ana ganin Najeriyar ma za ta zarce Jamus din wajen mamaye kudaden yankin.

Naira

Asalin hoton, AFP

Amma Mista Belinga ya bayyana cewa yana ganin dama a duk irin wannan lamari dole a samu jagora kuma Najeriya za ta iya kasancewa jagorar.

Ya ce hakan raguwar matsala ce kuma dama ce ga kasar domin samun kasuwa da kuma budi ga tattalin arziki.

Ya kuma ce yana ganin Najeriya za ta taka rawar gani musamman ganin yadda kasar ta habaka tattalin arzikinta, ya ce yana ganin alamun jagoranci na gari ga Najeriyar.

Fassara: Mustapha Musa Kaita