Sabuwar Shekara: Za a haifi yara 30,400 a Najeriya da Ghana da Kamaru yau- Unicef

Asalin hoton, Getty Images
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef ya ce yana sa rai za a haifi jarirai 25,685 a Najeriya ran daya ga Janairun sabuwar shekarra 2019.
Sabbin alkalumman da Unicef ta fitar sun ce Najeriya ce ta uku a jerin kasashe masu yawan haife-haife a duniya.
A Indiya da China ne kawai za a haifi yara fiye da Najeriya a wannan shekarar a cewar rahoton.
Rahoton ya kara da cewa za a haifi jarirai 2926 a Ghana, a Kamaru kuwa za a haifi 2517.
Haka kuma, UNICEF ya ce iya tsawon ran da ake sa rai yaron da aka haifa a Najeriya zai yi bai wuce shekara 55 ba, wato ba a sa rai jaririn da aka haifa a bana zai zarce shekara ta 2074.
Kasashen da za a fi haihuwar jarirai
- Indiya — 69,944
- China — 44,940
- Najeriya — 25,685
- Pakistan — 15,112
- Indonesia — 13,256
- Amurka — 11086
- Jamhuriyar Demokradiyyar Congo — 10,053

Asalin hoton, Getty Images
Pernilla Ironside, jami'a a Unicef ta ce "Za mu iya ganin cewa yaran da aka haifa a Najeriya sun rayu har su tsufa.
"A Najeriya, duk shekara kusan jarirai 262,000 ne ke mutuwa da an haife su kuma wannan shi ne na biyu mafi yawa a duniya."
"Kuma kullum a najeriya, jarirai 257 na mutuwa a cikin watan da aka haife su," in ji Permilla Ironside.
Mafi yawan abubuwan da ke kashe yara suna jarirai abubuwa ne da za a iya karewa kamar samun matsaloli a lokacin nakuda da cututtuka irinsu limoniya.











