Da gaske ne Buhari ya kori gwamnan CBN?

Asalin hoton, Getty Images
A farkon makon nan ne shafin Facebook na Hope For Nigeria ya ruwaito wani labari da ke cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele daga aikinsa.
Shugaba Buhari ya kori Mista Emefiele kuma ya zabi sunayen mutum biyu daga yankin arewacin kasar don zabar wanda zai maye gurbinsa daga cikinsu, kamar yadda labarin ya yi ikirari.
Labarin wanda aka yada sau fiye da 2,500, ya ce "Shugaba Buhari ya umarci Gwamnan CBN Godwin Emefile da ya tafi hutun aiki ne" domin maye gurbinsa da wani.
Wani tsohon daraktan sadarwa ga tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Jackson Ude, shi ma ya wallafa labarin a Twitter, inda aka yada shi sau sama da 500.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Mene ne gaskiyar labarin?
Dokar da ta kafa bankin CBN ta shekarar 2007 ta tanadi cewa shugaban kasa ba shi da ikon cire gwamnan CBN har sai ya samu sahalewar biyu cikin uku na mafi yawan 'yan majalisar dattawa.
Wa'adin Gwamnan CBN na shekara biyar zai kare ne ranar 3 ga watan Yunin shekarar 2019.
Mai magana da yawun CBN Isaac Okorafor ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa labarin "kanzon-kurege ne", inda wani ma'aikacin bankin kuma ya ce "gwamnan yana ofis a ranar Litinin kuma ranar Talata ma ya gana da manoman auduga."
Garba Shehu mai magana da yawun fadar shugaban kasar Najeriya ya ce babu gaskiya a labarin, saboda haka "na boge ne".

Menene labaran karya?
Sun kunshi bayanai na karya da hotuna da na bidiyo da ake kirkira a yada domin a harzuka mutane.
Ko kuma yada tsoffin hotuna, ko hotunan da ba ma a kasar aka dauka ba.
Irin wadannan labaran karyar da kuma hotunan karyar da ake yadawa, na taimaka wa wajen rura rikici musamman a tsakanin kabilu.
A wasu lokuta rashin samun bayanai daga bangaren gwamnati ko mutanen da abin ya shafa, na haifar da yada jita-jita da kuma zaman dar-dar.

Irin wadannan labaran karya kan haifar da illoli masu yawa, kamar tayar da fitina, da kulla kiyayya tsakanin al'umma da kuma yada bayanan da ba su da tushe.
Binciken da BBC ta yi a kwanakin baya ya gano cewa labaran karya na sahun gaba wurin yada rikicin da ake fama da shi a Najeriya tsakanin makiyaya da manoma.
Hakan ne kuma ya sa ma'aikatar sadarwa ta kasar kaddamar da wani shiri na musamman domin yaki da wannan dabi'a, wacce ke kara samun gindin zama a kasar, musamman a shafukan sada zumunta.
Yadda ake gane labaran karya
Akwai yiwuwar ci gaba da samun labaran karya kan wannan rikici, musamman a lokutan zabuka a Najeriya.
Kamfanonin sada zumunta kamar Twitter da Facebook sun bayyana shirinsu na yakar sana'ar yada labaran karya a duk fadin duniya, amma ga wasu hanyoyi biyar da za ka iya kawar da yada bayanan da ba su da tushe:

Asalin hoton, AFP
Binciki asalin labarin: Shafukan sada zumunta na karya kan yi kokarin bayyana kansu a matsayin cewa sun fito ne daga manyan kafofin watsa labarai, a don haka ka duba shafi sosai kafin ka watsa bayanan da suka wallafa.
Shafukan da aka tabbatar da halaccinsu suna dauke da alamar shudi a Facebook, da Twitter da kuma Instagram.
Duba wasu karin hanyoyin: Duk da cewa wannan wani lokaci ba zai gamsar ba amma yana da kyau a duba abin da wasu kafofin watsa labarai masu inganci ke cewa kan labari domin tabbatar da gaskiyar batu.
Tambayi kanka, shin ingantattun kafafan yada labarai na bada rahoton wannan labarin?
Hanyoyin bincika labari: Akwai hanyoyi da dama da za su taimaka maka wurin tabbatar da sahihancin hoto ko bidiyo. Google, da Bing da kuma Tin Eye duk suna duba asalin hoto, wanda kan iya gaya maka inda aka dauki hoto da kuma asalinsa. T
abbatar da bidiyo ya fi wahala amma shafuka kamar InVid na bada damar gano inda aka yi amfani da bidiyon da aka wallafa a Facebook da YouTube a baya.
Duba asalin abin: Idan kana da ainahin hoton ko bidiyo, za ka iya samun bayanai masu muhimmanci game da su, ciki har da wuri da kuma lokacin da aka dauka da kuma na'urar da aka yi amfani da ita.
Abin takaicin shi ne da zarar an wallafa hotuna a shafukan sada zumunta to bayanansu na sali sai su bace.
Yi tunani kafin ka wallafa: Dole a yi taka-tsan-tsan saboda ka da a kara jefa mutane cikin rudani. Kafin ka wallafa, ka tambayi kanka ko bayanan da ka ke da su sun inganta kuma ya karfin sahihancinsu yake.











