Dalilin da ya sa darajar naira ke ƙaruwa da amfanin hakan ga talaka

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Ƙwararru kan harkokin tattalin arziki na hasashen darajar naira za ta ci gaba da ƙaruwa a cikin mako mai zuwa sakamakon matakan da Babban Bankin Najeriya CBN ke ɗauka da kuma raguwar buƙatar kuɗaɗen ƙasar waje.
Zuwa ranar Alhamis da ta gabata, nairar ta farfaɗo a kasuwannin hukuma da na bayan fage, inda aka canzar da dala ɗaya kan N1,455 a duka kasuwannin.
Yanayin ya zo daidai da manufar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta APC wajen daidaita farashin dalar a kasuwannin biyu tun bayan da ta sauya tsarin hada-hadar a watan Yunin 2023.
Masana na alaƙanta farfaɗowar darajar nairar da dalilai da dama, yayin da ɗaiɗaikun 'yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar tsadar kayayyaki.
Wace irin farfaɗowa nairar ta yi?

Asalin hoton, Reuters
Bayanai daga Babban Bankin Najeriy CBN sun nuna cewa a ranar Alhamis da ta gabata, darajar naira ta ƙaru da kashi 1.4 cikin 100 a kasuwar hukuma, inda aka canzar da dala ɗaya kan N1,455.23 idan aka kwatanta da N1,475.34 da aka canzar da ita ranar Talata 30 ga watan Satumba.
A kasuwar bayan fage kuma, nan ma darajar nairar ta ƙaru da kusan naira 40 (kashi 2.7 cikin 100) bayan rufe kasuwar dala tana kan N1,455 idan aka kwatanta da N1,495 da aka canzar da ita ranar Talata.
Duk da cewa nairar ta yi daraja a ranar Alhamis, zuwa Juma'a ta ɗan ragu a kasuwar bayan fage da ta hukuma. Kafin rufe kasuwar a jihar Kano da ke arewacin ƙasar, an canzar da ita kan N1,450, yayin da aka canzar kan N1,466 farashin gwamnati.
Ma'ana, farashin kasuar bayan fage ya fi na gwamnati sauƙi, kuma shi ne abin da gwamnati ke son gani saboda a cewarta, hakan zai rage yawan neman kuɗaɗen waje da ake yi.
"Dangane da faduwar darajar dala, kusan sati biyu kenan a kowace rana tana karyewa," kamar yadda shugaban ƙungiyar 'yancanji ta Kano, Sani Salisu Dada, ya shaida wa BBC.
Farashi mafi muni da naira ta taɓa fuskanta shi ne a a watan Fabrairun 2024, lokacin da aka canzar da ita kusan N1,900 kan dala ɗaya.
Me ya sa nairar ke farfaɗowa a yanzu?

Asalin hoton, EPA
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tsawon shekaru, Najeriya na amfani da tsaruka na canjin kuɗi daban-daban, wanda ke jawo wagegen giɓi tsakanin kasuwannin bayan fage da kuma na hukuma.
Kafin marigayi Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki a watan Mayun 2023, akan canzar da naira kan N450 a kasuwar hukuma, da kuma N700 ko fiye a kasuwar bayan fage.
A lokacin, 'yan ƙalilan ne waɗanda ke da alfamar samun dala a kan farashin hukuma.
Tsarin barin kasuwa ta yi halinta da gwamnatin Tinubu ta ɓullo da shi bai yi wani tasiri nan take ba, inda har zuwa Fabrairun 2024 nairar ta gamu da mummunar faɗuwa zuwa kusan 2,000 kan dala ɗaya.
Dr Abdulrazak Fagge, masanin kimiyyar kasuwanci a Najeriya, ya ce faɗuwar darajar dala duk duniya ne.
"Ba a Najeriya ne kaɗai ba. Tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaƙaba haraji kan wasu kasashe, hakan ya haifar da martani daga wadannan kasashe." in ji shi.
Masanin ya ce CBN ya yi amfani da wannan damar, inda ya sayar wa 'yan kasuwar canji dala a wannan makon, wanda hakan ya ƙara karya darajarta tare da ƙarfafa darajar naira.
Ƙarin dalilan da za su sa darajar dala ta yi ƙasa a Najeriya sun haɗa dawo da tsarin bai wa 'yan Najeriya damar yin amfani da katin ATM ɗinsu na naira wajen sayayya ko biyan kuɗi a dala na kimanin dala 4,000 sau uku a shekara, wanda wasu bankunan kasuwanci ke aiwatarwa a yanzu.
Ko za ta ɗore?
Dr Abdulrazak Fagge ya ce naira na cikin kuɗaɗen Afirka da ake sa ran za su ci gaba da farfaɗowa a kan dala a cikin mai zuwa.
"gaskiya ba lallai ba ne ya ɗore," in ji Dr Abdulrazak Fagge.
Shi ma shugaban 'yankasuwar canji a Kano, Sani Salisu Dada, ya ce duk da cewa farashin kasuwar bayan fage ya fi na gwamnati sauƙi ranar Juma'a, hakan ba ya nufin haka za a ci gaba da tafiya.
"Babu yadda za a yi farashin bayan fage ya fi na gwamnati sauƙi, kawai razani ne da mutane ke da shi a yanzu waɗanda suke da dalar a gida suna fitowa da ita suna kawowa kasuwa," a cewarsa.
Ya ce hakan yana jawowa farashinta ya yi ƙasa.
Mene ne amfanin hakan ga talakan Najeriya?

Asalin hoton, Reuters
Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da ta dogara da kan abubuwan da ake shigarwa daga ƙasashen waje.
Baya ga abubuwan da suka shafi ayyukan gida, da ƙawata gidan, hatta kayayyakin abinci kamar shinkafa da aka fi ci a ƙasar, ana shigar da ita daga ƙasar waje.
Dr. Shamsuddin Muhammad malami ne a Tsangayar Tattalin Arziki ta Jami'ar Bayero ta Kano, kuma ya ce duka waɗannan abubuwan da ake shigarwa ƙasar da dala ake sayo su.
"Ka ga kenan idan darajar dala ta ragu kayayyakin za su yi wa 'yankasuwa sauƙi, su kuma za su rage farashi, talakawa kuma su saya da sauƙi," in ji shi.
"Haka nan, su ma masu sayo kayayyakin da suke sarrafawa domin yin wani abu a nan cikin gida, ko kuma kayan aikin sarrafawar, su ma za su samu ragin kuɗin da suke kashewa wajen sarrafa su, wanda zai sa su rage farashin nasu kayan."
Sai dai kuma akwai ƙalubale.
"Su kuma masu sarrafa kaya a cikin gida ba su buƙatar dala wajen sayo kaya, za su iya fuskantar asara," kamar yadda masanin ya bayyana.
"Saboda idan kayan ƙasar waje suka fi na gida sauƙi to mutane za su fi sayen na wajen, saboda da ma na gidan ba su kai ingancin na wajen ba."










