Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gwamnatin Zamfara ta yi bayani kan dalilan rufe kasuwannin dabbobi
Gwamnatin jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya ta bayyana dalilin rufe wasu kasuwannin dabbobi a jihar.
A ranar Laraba ne gwamnatin jihar ta sanar da rufe kasuwannin a kananan hukumomi bakwai waɗanda ta ce ana hada-hadar shanu da dabbobin sata.
Mannir Haidara Kaura, kwamishinan watsa labarai da raya al'adu na jihar, ya bayyana wa BBC Hausa cewa an dauki wannan mataki ne a wani yunkuri na tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama'ar jihar.
Ya ce bayanan da gwamnati da hukumomin tsaro suka samu sun nuna cewa yan fashin daji na shigo da dabbobin da suka kwace a hannun mutane suna cinikinsu inda suke samun kudin da suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
''Yanayi na tsaro abu ne da ke da sarkakiya, amma dai muna ganin matakan da wannan gwamnati ke dauka za su fara tasiri ba da jimawa ba, domin za mu toshe musu wannan kofa'' in ji kakakin gwamnatin
Ba dai wannan ne karon farko da gwamnatin jihar ta Zamfara ke rufe kasuwannin dabbobi ba, bisa zargin hada-hadar dabbobin sata da yan fashin daji ke kawowa.
A watan Satumba ma akwai wasu kasuwanni guda bakwai da gwamnatin jihar ta rufe saboda irin wannan zargi, inda ake ci gaba da bincike.
Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, inda yan fashin daji ke kai hare-hare, suna kashe jama'a da kuma satar dukiyoyinsu, ciki har da dabbobi.
Sai dai gwamnatin jihar na ganin cewa irin wadannan matakai da take dauka, za su taimaka wajen shawo kan matsalar da ta ki ci ta ki cinyewa.