Za mu kawar da matsalar tsaro zuwa ƙarshen 2024 – Matawalle

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta fahimci girman ƙalubalen tsaron da ke gabanta tare da alƙawalin kawo ƙarshen matsalar zuwa karshen 2024.

Gwamnatin ta ce a yanzu za a bi salon yaƙar ƴan bindiga da suka addabi ƙasar musamman yankin arewaci tun kafin su kaddamar da hari.

Ƙaramin ministan tsaro ne Dr Bello Muhammad Matawalle ya bayyana haka a hirarsa da BBC.

Ƴan bindiga masu muggan makamai sun daɗe suna ta’adi a Najeriya musamman yankin arewa maso yammacin ƙasar, inda suke kashewa da yin garkuwa da dubban mutane – lamarin da ke haifar da fargaba ga matafiya da kuma hana yin noma a wasu yankuna.

Wani rahoton kamfanin tsaro na Beacon Consulting a Najeriya ya ce sama da mutum 5,000 aka kashe a Najeriya daga watan Mayu da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya karɓi madafan iko.

“Idan Allah Ya yarda daga nan zuwa watan 11 na 2024 duk wasu matsaloli na tsaro za a shawo kansu,” kamar yadda ƙaramin ministan tsaron na Najeriya Dr Bello Matawalle ya shaida wa BBC.

Ya ce matakai da dubarun da yanzu ake ɗauka za su taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar.

Ya ce matakan sun haɗa da bin ƴan bindiga a gidajensu tun kafin su kai hari a murƙushe su.

Za mu yi sulhu ga masu son sulhu

Ƙaramin ministan wanda tsohon gwamnan Zamfara ne mai fama da hare-haren ƴan bindiga, duk da bai kawar da matakin sulhu ba amma ya musunta zargin cewa gwamnatin tarayya na yin sulhu da ƴan bindiga ta bayan fage.

Ya ce mutane ba su fahimci abin da ake nufi da sulhu ba. A cewarsa akwai ƴan bindigar da suka yarda da sulhu kamar waɗanda ya taɓa sulhu da su zamanin da yana gwamnan Zamfara.

Ministan ya ce tsarin da suka yi yanzu “duk wanda bai yarda da zaman lafiya ba, za a yaƙe shi."

'Gwamnan Zamfara ya zo mu haɗa kai'

Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da matsalar hare-haren ƴan bindiga ta yi ƙamari a arewa maso yammacin Najeriya. Jihar kuma ta yi fama da rikicin siyasa, wanda wasu ke ganin yana tasiri ga ƙoƙarin shawo ƙarshen matsalar tsaron.

Tun kayar da shi zaɓen gwamna a jihar Zamfara, ƙaramin ministan tsaron Bello Matawalle ya fara cacar-baki da gwamnan da ya gaje shi Dr Dauda Lawan Dare na jam’iyyar hamayya ta PDP kan zargin rashawa da wawushe kuɗaɗen jihar.

Ministan ya ce duk da girman ƙalubalen tsaron jihar amma a cewarsa, “gwamnan jihar bai taɓa tuntuɓarmu ba da ni da Badaru ko neman ya gana da mu kan matsalar tsaron jiharsa”

Ya ƙara da cewa gwamnoni da dama da ke fama da matsalar tsaro sun kawo masu ziyara domin haɗa kai da gwamnatin tarayya don shawo kan matsalar.

“Don haka ni ina kira ga nawa gwamnan ya nemi haɗin kan jami’an tsaro da gwamnatin tarayya domin aikin ba zai iya yi shi kaɗai ba.”

“Kada ya dibi shi tsakanin shi da ni, ya dibi al’ummar jihar Zamfara, a ajiye duk wani abu na siyasa a dawo mu haɗa kai domin samar da mafita ga jihar.

Hare-haren na ƴan bindiga dai a Najeriya babban al’amari ne da ya jefa jami’an tsaron ƙasar cikin rudani, inda hankalinsu ya rabu musamman yadda suke tunkarar ƴan’awaren yankin kudu maso gabas da rikicin makiyaya da manoma a jihohin tsakiyar kasar da aka shafe shekaru, ga kuma mayaƙa masu da’awar jihadi na Boko Haram da Iswap a arewa maso gabashin Najeriya.