Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha tsawon wata shida

Sanata Natasha Akpoti Uduaghan

Asalin hoton, Natasha/Facebook

Lokacin karatu: Minti 4

Majalisar dattawan Najeriyar dai ta ɗauki matakin dakatar da sanatar ne har na tsawon watanni shida bisa shawarwarin da kwamitin Ɗa'a da Ladabtarwa da Sauraron ƙorafin Jama'a na majalisar ya bayar, bayan nazari kan ƙorafin da sanata Natasha ta miƙa wa majalisar ranar Laraba.

Shugaban kwamatin, Sanata Neda Imasuen shi ne ya bayar da shawarwarin bayan karanto jerin laifuka da kwamitin ya ce ya samu Sanata Natasha da aikatawa a majalisar.

Da yake karanta bayanin dakatarwar, shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio wanda a kansa ne Sanata Natasha ke ƙorafin cin zarafi na lalata, ya nemi jin ra'ayin ƴan majalisar kan su amince ko su ƙi amincewa da dakatarwar ta tsawon watanni shida amma kuma za a iya rage yawan lokacin idan har ta rubuto takardar neman afuwa. Ƴan majalisar kuma sun amince da hakan.

Da ma dai tunda farko sai da kwamitin na Ɗa'a da Ladabtarwa da Sauraron ƙorafin Jama'a na majalisarya yi watsi da ƙorafin sanata Natasha bisa dalilan cewa ƙorafin da Sanata Natasha ta shigar ranar Laraba bai cika ƙa'ida ba saboda ita mai ƙorafin da kanta ta sanya hannu kan ƙorafin maimakon ta bai wa wani ya shigar da shi a madadinta, lamarin da ya ce ya lalata ƙorafin nata tun ba a je ko'ina ba.

Ya kuma ƙara da cewa batutuwan da ke cikin ƙorafin na gaban kotu a yanzu haka, wanda ya sa ba za a iya tattauna su ba kuma majalisar ba ta da hurumin sauraron su.

Kafin dai shugaban majalisar ta dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya sanar da dakatar da Sanata Natasha sai da aka bai wa ƴan majalisar dattawan da dama suka faɗi albarkacin bakinsu inda ba tare da ragin ɗaka ba suka goyi bayan hukuncin.

Sai dai shugaban marasa rinjaye na majalisar ta dattawa, Sanata Patrick Abba Moro na jam'iyyar PDP wanda shi ma ya ƙwanƙwashi Sanata Natasha amma ya nemi majalisar ta yi wa ƴar majalisar sassauci inda ya ce a rage tsawon lokacin dakatarwar daga watanni shida zuwa uku.

Sanata Natasha ta yi wuf ta ce "wannan rashin adalci ba zai ɗore ba", kafin a kashe abin maganarta.

Mene ne ƙorafin Sanata Natasha?

Sanata Natasha Akpoti

Asalin hoton, Channels/Screen grab

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sanata Natasha Akpoti Uduaghan, ƴar majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar jihar Kogi ta gabatar da ƙorafi a gaban majalisar dattawan ƙasar kan shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio.

Bisa rakiyar mai gidanta wanda ya rakata har ƙofar shiga zauren majalisar ta dattawa, Sanata Natasha Akpoti ta gabatar da ƙorafin nata kamar haka:

"Ina gabatar da ƙorafi da sunana kan shugaban majalisar dattawan Najeriya, mai girma Sanata Godswill Akpabio bisa cin zarafi na lalata da amfani da ofishinsa wajen tursasawa da kuma daƙile min aikina na ƴar majalisa bisa ƙeta."

"Za ka iya tunawa yallabai cewa a ranar Juma'a na yi wasu kalamai kuma yanzu na yanke shawarar taƙaice waɗannan kalamai zuwa ƙorafi kan shugaban majalisar dattawa,. Idan ka amince zan zo bisa girmamawa na ajiye wannan ƙorafi." In ji Sanata Natasha.

Daga nan ne Sanata Natasha ta sauka daga kujerarta da ke sama zuwa gaban shugaban majalisar inda ta rusuna sannan ta ajiye takardun ƙorafin.

Abin da ya janyo tankiya

Sanata Natasha ta zargi Sanata Akpabio da ƙoƙarin daƙile mata dama ta ƴar majalisa.

Asalin hoton, NIGERIAN SENATE/FACEBOOK

A ranar 20 ga watan Fabrairu ne dai tankiya ta ɓarke a zauren majalisar dattawan tsakanin shugaban majalisar, Godswill Akpabio da sanata Natasha Uduaghan da ke wakiltar tsakiyar jihar Kogi.

Rikicin ya samo asali ne lokacin da mai tsawatarwa na majalisar, sanata Mohammed Munguno ya shaida wa ƴan majalisar cewa sanata Natasha ta ƙi amince wa ta koma sabuwar kujerar da aka ware mata.

Al'amarin dai ya janyo har shugaban majalisar, Akpabio ya umarci ɗaya daga cikin masu yi wa sandan majalisar hidima da ta fitar da sanata Natasha daga zauren majalisar.

Hakan ne ya janyo ƙungiyoyi da mutane da dama yin kiraye-kirayen a yi bincike wani abu da ya sa majalisar dattawan ta nemi da Natasha ta je ta bayar da bahasi.