'Akwai buƙatar gudanar da binciken babu sani ba sabo kan zargin Sanata Natasha'

Asalin hoton, NEWSPAPER
Ana ci gaba da samun ƙarin ƙungiyoyi da jiga-jigan ƴan siyasa da ke yin kira da a gudanar da cikakken bincike kan babban zargin da wata Sanata ta yi wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio a kan cewar ta ƙi ba shi haɗin kai, shi ne yasa ya ke yi mata bita da ƙulli.
Sanata Natasha Akpoti Uduaghan daga jihar Kogi ta yi wannan babban zargin ne jim kaɗan bayan da aka soma kai ruwa rana tsakaninta da Sanata Akpabio, lamarin da yasa a yanzu majalisar dattawa ke binciken Sanata Natasha bisa zargin nuna rashin ɗa'a.
Ita dai Sanata Natasha ta nuna tirjiya bayan da aka sauya mata wurin zama a zauren Majalisar dattawa inda ta yi zargin cewa matakin na da nufin rufe mata baki tare da kawo mata cikas wajan gudanar da aikinta.
Saboda irin ƙurar da ta tayar sai Majalisar ta yanke shawarar cewa Sanatar ta jihar Kogi ta bayyana a gaban kwamitin ɗa'a domin ta kare kanta.
Kafin lokacin bayyana a gaban kwamitin sai sanatan ta je gidan talibijin na Arise inda ta yi zargin cewa shugaban Majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya 'nemeta domin lalata' kuma ba ta ba shi haɗin kai ba, shi ne abinda ya janyo ya sa mata ƙahon zuƙa har aka sauyamata wurin zama.
Sanata Natasha ta kuma maka shugaban Majalisar dattawan gaban kuliya inda take neman diyya saboda zargin ɓata mata suna
A ɗaya ɓangaren kuma matar Sanata Akpabio ta fito fili ta kare mijinta inda ta yi watsi da zargin cin zarafin da Sanata Natasha ta yi wa mijinta, kuma ta ce shairi ake neman ƙullawa mijinta.
A nasa ɓangaren mai gidan Sanata Natasha, wanda basarake ne a jihar Delta wanda ya shiga maganar a baya, ya ce ya taba jan kunnen shugaban Majalisar dattawan Najeriya a kan cewa ya daina shi-shige wa matarsa kuma daga bisani a cewarsa matarsa ta bayyana masa cewa Sanata Akpabio be ji wannan maganar ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A yanzu dai manyan ƴan siyasa sun shiga maganar kamarsu tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da kuma tsohon shugaban Majalisar dattawa Bukola Saraki waɗanda ke cewa akwai buƙatar gudanar da binciken ba bu sani ba sabo domin gaskiya ta yi halinta.
Suma masu rajin kare haƙƙin biladama da ƙungiyoyin kare ƴancin mata a Najeriya sun ce akwai haƙƙin da ya rataya a wuyar Majalisar dattawan ƙasar na gudanar da binciken da zai warware duk wata sarƙaƙƙiyar da ke tsakanin ƴar majalisar da kuma shugaban Majalisar dattawan.
Barista Hassana Maina lauya ce mai zaman kanta a Najeriya kuma shugabar ƙungiyar kare haƙƙin mata mai suna Anti Sexual Violence lead supportive initiative ta shaidawa BBC cewa sun yi wannan kiran ne domin kare kimar Majalisar dokokin ƙasar:
''Wannan zargi da Sanata Natasha ta yi wa shi Akpabio abu ne da ya kamata a bincika a ga mene ne gaskiyar alamarin''
''Kuma idan za a yi wannan binciken ya kamata Sanata Akpabio ya bada wuri domin binciken ya gudana, domin Majalisar dokoki wuri ne da ya kamata ayi doka domin kare jama'a'' in ji ta.
Tun bayan zargin da Sanata Natasha ta yi kuma mijinta ya goyi bayanta har yanzu Sanata Godswill Akpabio be fito bainar jama'a ya yi martani ba. Sai dai matarsa ta kare shi da kuma mataimakin mai tsawatarwa na majalisar dattawa Santa Onyekachi Nwaebonyi wanda ya bayyana zargin a matsayin yarfen siyasa.













