Me ya janyo tankiya tsakanin sanata Akpabio da Natasha a zauren majalisa?

Asalin hoton, Natasha Akpoti-Uduaghan/Instagram
Tankiya ta ɓarke a zauren majalisar dattawan Najeriya ranar Alhamis tsakanin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da sanata Natasha Uduaghan da ke wakiltar tsakiyar jihar Kogi.
Al'amarin dai ya janyo har shugaban majalisar, Akpabio ya umarci ɗaya daga cikin masu yi wa sandan majalisar hidima da ya fitar da sanata Natasha daga zauren majalisar.
Gidan talbijin na AIT ya rawaito cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da mai tsawatarwa na majalisar, sanata Mohammed Munguno ya shaida wa ƴan majalisar cewa sanata Natasha ta ƙi amince wa ta koma sabuwar kujerar da aka ware mata.
Mai tsawatarwar ya ƙara da cewa dalilin da ya sa aka ba ta sabon wurin zama shi ne domin cike gurbin da wasu ƴan majalisar guda biyu suka samar bayan barin jam'iyyar hamayya zuwa mai mulki ta APC.
Abin da ya biyo baya
Mai tsawatarwar, sanata Mohammed Munguno ya kafa hujja da doka ta 24 da ta shida na majalisar dattawa da suka ba shi tare da shugaban majalisar iko na sauya wa wa ƴan uwansu sanatoci kujerun zama a kowane lokaci.
Ya ƙara da cewa kuma kowane ɗanmajalisar na da damar yin magana ne daga kujerar da yake zaune- saboda haka ɗanmajalisa ba shi da damar magana daga wani wurin zama ba nasa ba.
To sai dai ita kuma sanata Natasha ba ta amince da hakan ba, inda ta tashi daga wurin da aka ba ta na asali tana ƙoƙarin kafa hujja da dokar mai lamba 10 da ke nuna an karya mata ƴancinta na kasancewarta ƴanmajalisa.
Hakan kuma bai yi wa shugaban majalisar dattawan daɗi ba inda ya hana ta magana bisa dalilin cewa tana magana ne daga kujerar da ba tata ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rahotanni sun ce sanata Natasha wadda aka ce ta fusata ta zargin Akpabio da ƙoƙarin rufe mata baki da manufar hana ta damarta ta magana a zauren majalisar.
Sanata Natasha ta buga ƙafarta a ƙasa lokacin da take magana tana cewa ba za ta amince ba a mayar da ita ƙuryar zauren.
Ta ƙara da cewa babu abin da tsohon gwamnan na jihar Akwa-Ibom zai iya yi mata da ya wuce ya dakatar da ita daga zauren.
Natasha ta kuma ce ko da ma an dakatar da ita to za ta ci gaba da bautata wa al'ummar Kogi ta tsakiya da suka zaɓe ta da ma sauran matan Najeriya.
Sanata Natasha ta ƙara da zargin sanata Akpabio cewa yana nuna mata "wariya sannan ya raina ta tare da wulaƙanta ta."
"Ba na tsoron ka," kamar yadda ta faɗa wa Akpabio. Ka yi min duk abin da ka ga dama, amma ba zan bar wannan kujerar ba. Kuna son ku rufe min baki."
Ana cikin hakan ne sai wasu ƴan majalisar dattawan suka rinƙa ƙoƙarin kwantar wa da Natasha hankali tare da ba ta haƙuri, inda kuma daga bisani ta haƙuri ta yi shiru.
Sai dai kuma ƙoƙarin masu yi wa sandan majalisar hidima na ɗauke ta daga kujerar da ƙarfin tuwo bai yiwu ba sakamakon hanawa da wasu sanatoci suka yi.
Daga bisani wasu ƴan majalisar dattawan sun roƙi shugaban majalisar sanata Godswill Akpabio da ya yafe wa Natasha.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun irin wannan tankiya tsakaniya ƴan majalisar da shugaban majalisar dattawan ba.
Ko a watan Yulin 2024 sai da shugaban majalisar dattawan ya fito a bainar jama'a ya nemi afuwar sanata Natasha bayann ya fuskanci suka daga ƴan Najeriya bisa hantarar ta a yayin wani zama a zauren.
Wani bidiyo dai ya yi ta karakaina a shafukan sada zumunta ya nuna yadda Akpabio ya faɗa wa sanata Natasha da ta rufe bakinta idan bai ba ta iznin magana ba har ma ya ce faɗa mata cewa "zauren majalisar dattawa ba gidan rawa ba ne."
A baya-bayan nan ne kuma sanata Akpabio ya sa ƴar majalisar dattawa da ke wakiltar birnin tarayya Abuja ta fusata har ta fice daga zauren bisa zargin cewa suna ƙoƙarin rufe mata baki.
Ƴan Najeriya da dama dai a shafukan sada zumunta na zargin shugaban majalisar ta dattawa da rashin iya magana da kuma raina mata.







