Ko sojojin ƙasashen Turai da ke Ukraine za su iya kare ƙasar?

Asalin hoton, PA Media
- Marubuci, By Grigor Atanesian in London & Liza Fokht in Paris
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Russian
- Lokacin karatu: Minti 4
Yayin da Rasha da Amurka suka fara tattaunawa don kawo karshen yaƙin Ukraine, shugabannin Turai na tattauna hanyoyi da za su tabbatar da cewa yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin ta kai ga samun zaman lafiya mai ɗorewa.
Sai dai, masana harkar tsaro sun faɗa wa BBC cewa shirin samar da zaman lafiya zai zama babban kalubale da dakarun Turai suka fuskanta cikin shekara 30 da suka wuce.
Bayan sanarwar da Donald Trump ya yi cewa zai gana da Vladimir Putin - watakila a Saudiyya - bayan tattaunawa ta wayar tarho na tsawon sa'a ɗaya da rabi a makon da ya gabata, an fara nuna damuwa a Kyiv da kuma ƙawayenta a Turai na cewa cimma yarjejeniya ba tare da su ba, zai buɗe hanyar sake ɓarkewar sabon faɗa ko rikici a gaba a faɗin nahiyar.
Birtaniya a shirye take don tura dakaru zuwa Ukraine domin taimakawa wajen samar da tsaro a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiya, kamar yadda Firaiminista Sir Keir Starmer ya sanar ranar Lahadi, abin da ya dawo da batun da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya buƙata a bara.
Sai dai, bayan wani taron gaggawa da shugabannin Turai suka kira a Paris ranar Litinin, inda aka samu rabuwar kawuna kan batun, Sir Keir ya nanata cewa duk wata yarjejeniyar zaman lafiya za ta buƙaci Amurka ta dakatar da Rasha daga kaddamar da ƙarin hare-hare kan Ukraine.
Amurka ta yi watsi da batun aika dakarunta kuma ta nanata cewa alhakin tabbatar da tsaron Ukraine na karkashin Turai. Wannan ya janyo shakku kan cewa ko za a samu zaman lafiya ba tare da hannun Amurka ba.

Asalin hoton, PA Media
"Ban san ta ina za a samu yawan sojojin ba. Birtaniya za ta tura tare da kula da burget ɗaya, wanda zai kunshi sojoji kusan 5,000," a cewar Dr Frank Ledwidge, tsohon jami'in leƙen asirin Birtaniya wanda ya yi aikin wanzar da zaman lafiya a ƙasashen Bosnia da Kosovo.
"A Bosnia, ƙasar ta yi faɗin Ukraine sau goma, muna da masu wanzar da zaman lafiya 60,000, wanda ya kunshi da yawa daga Amurka da kuma Birtaniya. Sojojin Birtaniya ba su da yawa a lokacin kuma ba su da isassun makamai," in ji Dr Ledwidge .
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yanayin shirin wanzar da zaman lafiya da kuma ƙoƙarin Amurka - na cikin abubuwan da suka saka aka samu nasara a baya, in ji shi.
"A dukkan shirin wanzar da zaman lafiya da muka yi, suna tsoron mu, kuma ba mu da fargabar komai. Muna da tabbacin cewa Amurka na goyon bayan" kamar yadda Dr Ledgwidge ya tuna lokacin aikin zaman lafiya da suka je tsohuwar Yugoslavia.
"Wannan muhalli zai fi haɗari a kan wanda muka gani a Bosnia da Kosovo, kuma ina gani har da Iraqi da Afghanistan," kamar yadda jami'in ya yi gargaɗi.
"Ba za mu aika sojoji ba har sai mun tabbatar akwai ka'idojin kariya daga jirage marasa matuki, da kuma cewa sojojin da za a tura yawansu zai kai su bai wa dakarun mu kariya."
Duk da wannan damuwa, wasu na ganin cewa Birtaniya na da zimmar ganin an dama da Turai a samar da zaman lafiy. John Foreman, wani tsohon jami'in soja a ofishin jakadancin Birtaniya a Moscow, ya yi imanin cewa jagorancin Birtaniya zai saka wasu su bi baya.
"Birtaniya za ta iya aika dakaru kusan 10,000 zuwa Ukraine. Za mu yi wannan hobɓasa saboda ƙasashen Turai da ba su da karfi su shiga su ma," in ji shi.
Baya ga Birtaniya da Faransa, ba a san waɗanne ƙasashen Turai mambobin Nato da za su aika dakaru zuwa wanzar da zaman lafiya ba.
Da yake jawabi a taron da aka yi a Paris, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce "wannan ba lokaci ne da ya kamata a tattauna batun nan ba".
Sai dai maganar da Scholz ya yi kan lokacin - mai yiwuwa ya yi tasiri kan zaɓen da za a gudanar ranar Lahadi da kuma rashin matsaya kan tattaunawar zaman lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Turkiyya da ta kasance mamba a ƙungiyar Nato - ta biyu a yawan dakaru bayan Amurka, ba ta bayyana matsayarta kan yiwuwar aika sojoji ba. Makwafciyar Ukraine, Poland, wadda take ta uku a yawan sojoji, ta riga ta ce ba za ta tura dakarunta zuwa Ukraine ba.
Ba tare da waɗannan muhimman masu ruwa da tsaki ba, ƙwararru sun kiyasta cewa sauran mambobin Nato za su iya tura dakaru da suka kai 30,000 - wanda kuma ya yi kaɗan ga dubun-dubatar da shugaba Volodymyr Zelensky ya ce yana buƙata.
Wasu sun kalubalanci cewa samun iko da wani ɓangare na fagen daga, tare da taka rawar sojojin Ukraine, zai iya sanyawa a rage buƙatar dakaru masu yawa.
Ana sa ran Starmer zai kai ziyara Washington a mako mai zuwa don ganawa da Trump, inda ake tsammanin zai nemi goyon bayansa kan shirinsa.
Wani mai bayar da shawara kan harkokin waje kusa da shugaban Amurka, Fred Fleitz, ya fada wa BBC cewa "wannan abu ne mai kyau daga Firaiministan" kuma hakan zai zama "gudummawa mai muhimmanci".
Ko Rasha za ta amince da wannan shiri shi ne wani batu na daban.
Ministan harkokin wajen ƙasar Sergey Lavrov ya ce ba za su lamunci aika dakarun ƙasashen waje daga NATO zuwa Ukraine ba, ko da suna karkashin tutoci daban, inda ya yi gargaɗin cewa Moscow za ta kalli hakan a matsayin faɗaɗar ƙawance, abin da kuma ya sa Putin ya mamayi Ukraine.
A ɗaya gefen, ƙasashen Turai ba sa cikin tattaunawar zaman lafiya da ake yi, inda Rasha da jami'an Amurka ke ganawa a halin yanzu ba tare da su.
Muhimmin tambaya a yanzu ita ce ko Turai na da tasirin da za ta ja hankalin Amurka na ganin buƙatar tura dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa Ukraine idan aka samu tsagaita wuta a tattaunawar da ake yi a Saudiyya.
Zuwa yanzu dai, Rasha na ganin rawar da Turai ke takawa zai ƙara tsawaita yaƙi ne maimakon warware shi.











