Mene ne matsayin Abiola bayan kalaman IBB?

IBB

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Bayan kwashe fiye da shekara talatin da soke zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993 da gwamnatin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta lokacin ta yi, har yanzu batun nan tamkar an kashe maciji, amma ba a sare kan ba, sakamakon yadda kurwarsa ke ci gaba da tasowa.

Hatta a wajen kaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, da aka yi jiya Alhamis a babban birnin tarayya Abuja, shi ma da kansa tsohon shugaban Najeriyar, ya tabo batun soke wancan zabe.

Kuma Bala Ibrahim, wani mai sharhi kan al'amura, kuma tsohon ma'aikacin BBC, wanda ya halarci bikin, ya shaida hakan.

"Lallai a littafinsa ya bayyana haka kuma da ya zo jawabin godiya ya sake nanatawa ya yi nadama ya nuna cewa, koda yake ba a bayyana sakamako baki daya ba,amman sakamakon da ya zo hannu aka ƙidaya ya nuna cewa Cif Abiola na gaban abokin takararsa Bashir Tofa nesa ba kusa ba, don haka ana iya cewa MKO Abiola ne ya lashe wannan zaɓe." Cewar Bala Ibrahim.

Farfesa Usman Muhammad Shu'aib, tsohon shugaban tsangayar koyar da aikin lauya ta jami'ar Bayero ta Kano, a yanzu kuma daraktan cibiyar kula da hada-hadar kudi da bankunan musulunci ta jami'ar ya shaida wa BBC cewa Abiola yana nan a matsayinsa na wanda aka yi amannar ya lashe zaɓen 12 ga watan Yunin, 1993.

Lauyan ya bayyana wa BBC cewa ba za a iya kiran MKO Abiola da tsohon shugaban ƙasa ba saboda ba a ayyana shi a hukumance ba, "Dama binbinin abin yana nan ba mutuwa ya yi ba, ko lokacin mulkin Buhari, an canja ranar Dimokradiyya zuwa 12 ga watan Yuni."

To, ko hakan zai kawo karshen gutsuri-tsoma mai tangan da wutar kaikai, da ake ta yi, game da zaben 12 ga watan Yuni da aka soke a shekarun baya? Lokaci ne zai iya tabbatar da hakan.

A ranar 12 ga wata Yunin 1993, ɗan takarar SDP Abiola ya fafata da ɗan takarar NRC Bashir Tofa a zaɓen shugaban ƙasa. Abokin takarar Abiola shi ne Baba Gana Kingibe, inda Sylvester Ugoh ya zama mataimakin Tofa.

Duk da cewa masu sharhi na ganin zaɓen na 12 ga Yuni ya fi kowanne inganci, sai dai gwamnatin mulkin soja ta Ibrahim Badamasi Babangida ta soke shi bisa zargin maguɗi.

Matakin ya jawo ce-ce-ku-ce kuma daga baya Babangida ya sauka daga mulki a 1993. Ernest Shonekan, wanda ɗan garinsu Abiola ne, ya zama shugaban ƙasa na riƙo.

A ranar 11 ga Yunin 1994, Abiola ya ayyana kan sa a matsayin shugaban ƙasa a Legas, jihar da ke kudu maso yammacin ƙasar. Matakin nasa ya sa gwamnatin Sani Abacha ta soja ta zarge shi da cin amanar ƙasa kuma aka kama shi a ranar 23 ga Yunin 1994.

An tsare Abiola tsawon shekara huɗu, har ma wasu rahotanni na cewa ban da Ƙur'ani da Bibble masu tsarki ba shi da wata hanyar samun wasu bayanai.

Abiola ya rasu ranar 7 ga watan Yulin 1998, ranar da ya kamata a sake shi daga gidan yari.