Ƙorafin da Natasha ta gabatar wa majalisar dattawa kan Sanata Akpabio

Asalin hoton, NIGERIAN SENATE/FACEBOOK
Sanata Natasha Akpoti Uduaghan, ƴar majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar jihar Kogi ta gabatar da ƙorafi a gaban majalisar dattawan ƙasar kan shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio.
A ranar 20 ga watan Fabrairu ne dai tankiya ta ɓarke a zauren majalisar dattawan tsakanin shugaban majalisar, Godswill Akpabio da sanata Natasha Uduaghan da ke wakiltar tsakiyar jihar Kogi.
Rikicin ya samo asali ne lokacin da mai tsawatarwa na majalisar, sanata Mohammed Munguno ya shaida wa ƴan majalisar cewa sanata Natasha ta ƙi amince wa ta koma sabuwar kujerar da aka ware mata.
Al'amarin dai ya janyo har shugaban majalisar, Akpabio ya umarci ɗaya daga cikin masu yi wa sandan majalisar hidima da ta fitar da sanata Natasha daga zauren majalisar.
Hakan ne ya janyo ƙungiyoyi da mutane da dama yin kiraye-kirayen a yi bincike wani abu da ya sa majalisar dattawan ta nemi da Natasha ta je ta bayar da bahasi.
Abin da Sanata Natasha ta gabatar

Asalin hoton, Channels TV/ Grab
Bisa rakiyar mai gidanta wanda ya rakata har ƙofar shiga zauren majalisar ta dattawa, Sanata Natasha Akpoti ta gabatar da ƙorafin nata kamar haka:
"Ina gabatar da ƙorafi da sunana kan shugaban majalisar dattawan Najeriya, mai girma Sanata Godswill Akpabio bisa cin zarafi na lalata da amfani da ofishinsa wajen tursasawa da kuma daƙile min aikina na ƴar majalisa bisa ƙeta."
"Za ka iya tunawa yallabai cewa a ranar Juma'a na yi wasu kalamai kuma yanzu na yanke shawarar taƙaice waɗannan kalamai zuwa ƙorafi kan shugaban majalisar dattawa,. Idan ka amince zan zo bisa girmamawa na ajiye wannan ƙorafi." In ji Sanata Natasha.
Daga nan ne Sanata Natasha ta sauka daga kujerarta da ke sama zuwa gaban shugaban majalisar inda ta rusuna sannan ta ajiye takardun ƙorafin.

Asalin hoton, Channels Tv/Grab
Martanin Sanata Akpabio

Asalin hoton, FB/GODSWILL AKPABIO
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sanata Akpabio ya amince da buƙatar Sanata Natasha na ta gabatar da ƙorafin nata inda kuma bayan da ta ajiye kundin a gabansa, sai ya ce:
"Na miƙa wannan ƙorafi ga kwamitin majalisar dattawan mai kula da halayya da dabi'un ƴan majalisa da su yi nazari kansa su kuma dawo wa majalisar da bayani nan ba da jimawa ba."
Daga nan ne kuma sai Shugaban majalisar dattawan ya yi bayani cikakke ga sauran ƴan majalisar kamar haka:
"...dangane da wasu kalamai na ƙazafi da ke yawo a kafafen sada zumunta..na zargin cin zarafi na lalata da Sanata Natasha ta yi. Duk da cewa ina da cewa batun na gaban alƙali amma zan so na fayyace cewa babu lokacin da na taɓa yunƙurin cin zarafin Sanata Natasha da ma duk wata mace.
Mahaifiyarmu da ta rasu a shekarun farkon 2000 ta ba mu tarbiyya ni da ƴanuwana. Saboda haka ina martaba mata. Sannan ina son faɗin cewa ni ma ina da ƴaƴa mata huɗu kyawawa saboda haka babu lokacin da ci zarafin wata mace...
Kuma ko lokacin da nake gwamna, ni samu karramawa a matsayin gwamnan da ya fi kowa zama mai girmama mata ....Daga ƙarshe ina jan hankalin ƴan Najeriya musamman kafafen watsa labarai da ma ƴan soshiyal midiya da su jira hukuncin kotu kan batun maimakon yanke hukunci da kansu..." In ji Sanata Akpabio.
Natasha ba ta samu goyon bayan ƴan majalisa ba
Kusan ilahirin ƴan majalisar dattawan da suka yi tsokaci dangane da wannan ƙorafi da Sanata Natasha ta miƙa babu wanda ya goyi bayan ƙorafin, hatta sanatoci mata ƴan uwanta.
Da dama daga cikin sun yi nuni da cewa ƙorafin ma bai cancanci a gabatar da shi a zauren majalisar ta dattawa ba.
Wasu daga cikin ƴan majalsiar sun nemi da a shiga ganawar sirri domin tattauna batun duk kuwa da cewa shi shugaban Majalisar ta Dattawa, Sanata Godswill Akpabio wanda a kansa ne ake ƙorafin, ya ce hakan ba zai yiwu ba kasancewar akwai wakilai daga Burtaniya da suka je zauren domin ganin yadda al'amuran aikin majalisar ke tafiya.











