Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Hilda ta kafa tarihin girka shinkafa dafa-duka mafi yawa a duniya
Kundin bajinta na 'Guinness World Records' ya tabbatar cewa matashiyar nan yar Najeriya Hilda Baci ta kafa tarihin girka dafa-dukar shinkafa mafi yawa a duniya.
Hakan na zuwa ne bayan dubban mutane sun taru a ranar Juma'a 12 ga watan Satumban 2025 a birnin Legas, domin kallon yadda mai riƙe da kambin kundin bajintar kan girki ta gudanar da girkin shinkafa dafa-duka.
Dafa-dukar shinkafa da ake yi wa laƙabi da 'jollof' abinci ne da ya shahara a ƙasashen Najeriya da Ghana da Senegal da Saliyo da Laberiya da ma wasu da dama.
Hilda mai shekara 28 a duniya ta yi shuhura ne a shekara ta 2023 bayan kafa tarihin kwashe lokaci mafi tsawo tana girki ita kaɗai, na tsawon sa'a 93 da minti 11.
Wata sanarwa da kundin bajinta na Guinness ya fitar a ranar Litinin 15 ga watan Satumban 2025 ta ce Hilda Bacci ta yi nasarar girka dafa-duka irin ta Najeriya mafi yawa.
"An kafa sabon tarihi: Shinkafa dafa-duka mafi girma - 8,780kg (19,356 lb 9 oz) wanda Hilda Baci ta yi," kamar yadda kundin bajinta ya wallafa a shafinsa na X.
Hilda ta shaida wa BBC cewa abin da ya sa ta yanke shawarar yin wannan girki shi ne saboda "Najeriya ce a gaba a kodayaushe."
"Mu ne giwar Afirka, kuma na san cewa a matsayinmu na giwar Afirka dafa-dukanmu tana da mugun daɗi, zai yi kyau idan muka ɗora tukunyar dafa-dukan shinkafa mafi girma."
Wannan ne karo na farko da wani ya yi ƙoƙarin dafa shikafa dafa-duka mafi yawa.
Matasa da dama, da sanannun ƴan fim da mawaƙa ne suka yi dandazo a inda ake girkin domin nuna goyon baya ga Hilda Baci.
Hilda Baci ta shaida wa BBC cewa ta kwashe kimanin shekara ɗaya tana shirya yadda za ta gudanar da girkin.
Ta ce sai da aka kwashe wata biyu ana haɗa tukunyar dahuwar.
Ta bayyana cewa tukunyar girkin na iya cin lita 22,619, inda mutane da dama suka taru domin ganin abin ya tabbata. "Tawagar girkin ta kai yawan mutum 300."
Abubuwan da Hilda ta yi amfani da su wajen girkin su ne:
- Buhu 200 na shinkafar basmati,
- fiye da kilogiram 1200 na tumatur.
- Kilogiram 600 na albasa.
- Kilogiram 6000 na ruwa.
- Naman akuya kilo 168
- Man girki kilo 700.
Wace ce Hilda Baci?
A shekarar 2023 kundin bajinta na ''Guinness World Record'' ya bayyana Hilda Bacci a matsayin wadda ta kafa tarihin lokaci mafi daɗewa tana girki, bayan ta kwashe awa 93 da minti 11.
Wannan bajinta da ta nuna ya sa ta yi suna a ƙasar inda ta já hankalin sanannun mutane da ƴansiyasa.
"Girkin Hilda ya ja hankalin mutane ta yadda sai da shafinmu na intanet ya ɗauke na tsawon kwana biyu, sanadiyyar tururuwar mutane zuwa dalilin girkin Hilda," in ji shafin Guinnes.
Hilda ta yi girki ne na tsawon sa'o'i 100, inda ta riƙa hutawa na minti biyar bayan kowace sa'a ɗaya, sai dai kundin Guinness ya amince da awa 93 da minti 11 ne saboda a cewar sa ta huta a wasu lokutan fiye da yadda ya aminta.
Hilda ta yi karatu ne a jami'ar Madonna University, inda ta yi digiri kan ilimin halayyar ɗan'adam. Daga nan ne ta yanke shawarar zama mai sana'ar girke-girke.
Ta ce ta yanke wannan shawara ce domin yin koyi da mahaifiyarta, Lynda Ndukwe, wadda ita ma ƙwararriyar mai abinci ce.
Baci ta riƙa gabatar da wani shirin talabijin a shekarar 2020. Ta taɓa lashe gasar dafa shinkafa dafa-duka a shekara ta 2021, inda ta wakilci Najeriya.
A gasar ce ta doke Leslie Kumordzie daga Ghana domin zama zakara.