Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Dole ta sa nake girki da gawayi duk da illarsa ga lafiya da muhalli'
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist
- Lokacin karatu: Minti 6
Daga sallama, hayaƙin da ya turnuƙe tsakar gidan ne zai fara maka maraba. A gefe kuma a ƙarƙashin wata rumfa Malama Habiba ce a zaune a gaban murhun gawayi tana dafa ruwan zafi, a ɗayan kuma tana toya gurguru.
Tana aikin, tana ƙoƙarin sake rura wutar gawayin, lamarin da ke ƙara ɗaga hayaƙi da toka su baɗe mata fuska da jiki.
Habiba ta san amfani da gawayi yana tattare da illoli, domin a cewarta ta kwashe sama da shekara 10 tana amfani da shi a matsayin makamashin girki, har takan sara ta sayar.
Sai dai duk da zafin ƙirji da take fama da shi - alamar ciwon zuciya - da raɗaɗi wajen numfashi, ta ce shi ɗin ne dai makamashin da za ta iya mallaka.
Ba za ta iya sayen gas ko kalanzir ba - makamashin da ta ce na masu kuɗi ne - sannan ba ta da na'urar girki ta wutar lantarki, sannan kuɗin da take samu bai ma isa ta ciyar da ƴaƴanta da mijinta ya rasu ya bar mata da kyau ba, ballantana sayen wani makamashin.
Wannan ya sa ala dole gawayin ne kaɗai makamashin da ya rage mata a matsayin zaɓi, wataƙila saboda ya fi sauƙin farashi, kuma ya fi sauƙin samu.
"Ina ji a jikina cewa yana min illa domin ina jin zafi a ƙirjina, sannan ina shan wahala wajen numfashi," in ji Habiba a lokacin da take ƙoƙarin kakkaɓe murhun gawayin da take amfani da shi.
Amma ba Habiba ba ce kaɗai ke fuskantar irin wannan barazanar ba, domin dubban mata, musamman a arewacin Najeriya da wasu ƙasashen Afirka sun fi amfani da gawayi wajen girki.
Wannan bai rasa nasaba da talauci da rashin isasshiyar wutar lantarki, wanda yankunan Najeriya ke fama da su. Wannan ya sa duk da haɗarin da ke tattare da amfani da gawayin, wasu suka sadaukar da lafiyarsu domin su ciyar da iyalinsu.
'Gawayi kaɗai zan iya saya'
Habiba Muhammad haifaffiyar garin Bichi ce da ke jihar Kano, amma aure ya mayar da ita jihar Kaduna, duk a arewacin Najeriya.
Ta ce yanayin da ƙasar ke ciki ne ya tilasta mata amfani da gawayi, wanda a cewarta shi kansa gawayin ma na neman ya fi ƙarfinta a yanzu da ya fara tsada.
"Da ina saro itace ne, amma bayan rasuwar mijina, sai ya zama jarin ya karye, sai na koma ɗauko bashin buhunan gawayi, idan na sayar in kai kuɗin, in karɓo wasu. Wani lokacin ma kuɗin ba ya haɗuwa bayan na sayar da gawayin, sai dai in roƙa ina ƙara karɓar wasu, a hankali a hankali ina biya."
Ta ce ta daɗe tana sayar da gawayi kuma tana amfani da shi a gida. "Ko me zan yi da shi nake yi. Da girki da sana'ar da nake yi duk da shi nake amfani. A lokacin damina da sanyi ma ina kai shi ɗaki domin ɗumama ɗakin. Amma sai na lura idan na kai garwshi ɗaki nan da nan sai in ji kaina ya fara ciwo, kamar zan yi amai, kuma cikina na murɗawa."
A game da me ya sa ta zaɓi amfani da gawayi maimakon kalanzir da gas, sai ta ce, "Waɗannan ai na masu ƙarfi ne. Saboda Allah, kai da kake neman na abinci. Gawayin ma ba don albarkacin sayarwar ba, shi ma ɗin ai diddiga nake tankaɗewa in yi amfani da shi saboda idan na taɓa asalin gawayin, zan taɓa uwar kuɗin kuma na mutane ne."
Ta ce kuma ga hidimar ciyar da marayun da aka bar mata, "ciki ne zan saya abincin da zan ba marayuna, idan ina amfani da asalin gawayi, kuɗin mutane zai shige, ka ga ba zai yiwu ba."
Habiba ta ce ta daɗe tana samun labarin cewa amfani da gawayin yana jawo ciwon zuciya da wasu illolin, "amma amfani da shi ya riga ya zama dole. Ai babu yadda mutum zai yi. Dole ita ce hanyar sana'ar da za ka ɗan samu. Idan girkin ne ma da shi mutum zai yi. Ya mutum zai yi? Ya zama dole ne wani abun kana ji lalura ce amma in ba yadda za ka yi ya zama maka shi ne hanyar cin abincin. Dole ka haƙura."
'Yana min illa'
A game da yadda amfani da gawayin ke illa ga lafiyarta, Habiba ta ce tana ganin alama amma babu yadda za ta yi.
Ta ce, "Idan zan yi tari ko kaki, za ka gan shi baƙi ne. Yadda ka san an zuba gawayi a ciki. Sai kuma ciwon ƙirji. Zan riƙa ji kamar ina haki, musamman idan na juye buhun gawayi saboda ƙurar takan dawo ta baɗe min jikina," in ji ta.
Ta ce akwai wani yaronta da ƙafarsa ta farfashe, "a bara ƙafarsa ta farfashe saboda yawancin su ne suke taya ni aikin. Har yanzu akwai alamar a ƙafarsa, sai aka ce in daina barin sa yana shiga gawayin."
Sai dai ta ce ba ta taɓa zuwa asibiti ba, "Sai dai kawai in sayi maganina a kemis in sha."
"Idan na ajiye gawayin a ɗaki, ko idan muna girki da shi sai in riƙa jin ciwon kai. Dole sai na fitar da shi sannan in buɗe tagogi iska na shiga."
Amma Habiba ta ce da za ta samu dama, za ta daina amfani da makamashin gawayi, inda ta ce, "Kowa yana son ya samu hutu ko da ci gaba. Yanayi ne kawai saboda ka ga yanzu babu mijina ya rasu, nauyin makarantar yara da abincinsu da komai yana kaina ne. To ka ga duk wata sana'ar ta zama maka dole ne, kamar ta gawayin nan."
'Hayaƙi na kashe miliyoyin mutane duk shekara'
A wani lamar mai ɗaga hankali, shirin kula da muhalli na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ƙiyasta cewa hayaƙin da ake shaƙa wajen girki na kashe miliyoyin mutane duk shekara a faɗin duniya.
Shirin ya ce matsalar ta fi ƙamari a nahiyar Afirka, inda duk mutum huɗu cikin biyar ke fuskantar barazanar kamuwa da illa saboda hayaƙin na girki.
Haka kuma Hukumar makamashi ta duniya ta ce a Afrika, aƙalla kashi 60 na yara da mata na mutuwa sakamakon shaƙar hayaƙi.
Sannan kuma hukumar kula da yanayi ta duniya ta ce hayaƙin gawayi na ƙara illar sauyin yanayi.
"Illar hayaƙin gawayi ga lafiyar ɗan'adam"
Dr. Umar Sani Ibrahim, likita ne a fannin lafiyar al'umma a babban asibitn koyarwa na Barau Dikko da ke Kaduna, ya ce amfani da gawayi wajen girki babbar barazana ce ga lafiyar al'umma.
A tattaunawarsa da BBC Hausa, Dr Umar ya ce hayaƙin gawayi, musamman wanda aka samo daga itacen ɗanye ko mai laushi da ake kira "soft wood" na fitar da guba kamar "carbon monoxide", wanda ke shafar huhu da zuciya da ƙwaƙwalwa.
Ya ce yawan amfani da gawayi na iya haddasa cututtuka da dama irin su:
- Asthma
- Ciwon ƙirji
- Dajin huhu
- Ciwon zuciya da sauransu
Haka kuma, ya ce yara da mata masu ciki na fuskantar barazana ta musamman, saboda gubar na iya shiga cikin jini ya shafi jaririn da ke ciki.
Ya ƙara da cewa akwai wasu alamomi da ya kamata a lura da su:
- Jiri
- Ciwon kai
- Rashin isasshen numfashi
- Kasala
Ya shawarci jama'a da su guji amfani da gawayi a cikin ɗaki ko wuri maras iska, kuma idan an samu waɗannan alamomi, a garzaya asibiti maimakon zuwa shagon magani kawai.
A ƙarshe, ya buƙaci gwamnati da ƙungiyoyi su samar da hanyoyi masu sauƙi kamar samar da wutar lantarki da gas, da kuma wayar da kan al'umma game da illolin hayaƙin gawayi.
Illoli ga muhalli
A ɓangaren illar da gawayi ke yi ga muhalli, Abdullahi Abubakar Ladan, daraktan sadarwa na Gidauniyar Green Climate Africa, ya ce sare itatuwa da ake yi domin haɗa gawayi na illa ga muhalli da mutane da dabbobi.
Ya ce sare itatuwa da ake yi a dazuka ne suka sa dabbobi da dama suke tserewa suna ƙara matsawa saboda rashin dazukan ya sa ba za su iya rayuwa a wuraren da suke saba ba.
"A ɓangaren mutane kuma, daga cikin illolin da za mu iya gani, akwai yadda guguwa ke kwashe rufin gidajen mutane. Idan guguwa ta taso, idan akwai bishiyoyi, za su rage ƙarfinta."
Ya ƙara da cewa bishiyoyi suna musayar iska da mai kyau da gurɓatacciya da mutane, domin "iskar da muke shaƙa guba ce a wajen bishiya da tsirrai, mu kuma wanda muke fitarwa shi suke so. Don haka sai a yi musaya."
Ya kuma ce riƙe ruwa da bishiya ke yi na rage zafin yanayi a cikin muhalli.