Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sauyin yanayi: Yadda ƙwararru ke ƙoƙarin ceto duniya daga gurɓacewar muhalli
- Marubuci, Daga Matt McGrath
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Environment correspondent
Yanzu haka, a yayin da kuke karanta wannan makala, wasu masana kimiyya 200 a fadin duniya na aiki ba-dare-ba-rana don tantance wani rahoto da zai sauya yanayin duniya.
Tun a shekarar 2013 ne kungiyar gwamnatoci kan sauyin yanayi (IPCC) ke gudanar da cikakken bincike kan dumamar yanayi na duniya.
A makonni biyu masu zuwa, za su dudduba sakamakon binciken nasu daya-bayan-daya tare da kare kowane bangare na kimiyyar yanayi ga sauran 'yan tawagar masana kimiyya da masu mulki.
Takaitattun bayanai da mahukunta suka samu na kusan shafuka 40, za su taka muhimmiyar rawar yi wa shugabanninin kasashe jagora wajen fuskantar muhimman tambayoyi game da yanayi da hakan zai sauya tarihin duniya - da ka iya kasancewa sauyi mafi kyau.
Kwararru sun ce rahoton zai kasance ''matashiya'' ga gwamnatoci - kuma an wakilci kasashe 195 a zaman tattaunawar da tawagar kungiyar ta IPCC ke gudanarwa.
Wakilin BBC kan harkokin muhalli Matt McGrath ya duba wannan muhimmiyar kasida da ake kan gabatarwa - dalilan da suka saka ta kasance mafi muhimmanci a cikin kusan shekara 10, da kuma dalilan da suka saka ya kamata mu damu da ita.
Mene ne sabo a cikin rahoton binciken na shida?
A lokutan baya, IPCC ta fitar da rahoto mai kama da wannan, har yanzu hasashen yanayin na da sahihanci matuka, kana narkewar tuddan kankara a yankin Siberia na ƙasar Rasha bai yi tsananin da aka yi tsammani ba.
A cikin wannan shekarar, tawagar ta sake komawa zamanta a yayin da tsananin zafi ya girgiza kasashen Amurka da Canada da Turai da kuma yankin Asiya.
An kuma ɗiga ayar tambaya mai girma fiye da yadda aka saba kan rawar da sauyin yanayin da ɗan Adam ke haddasawa.
Kamar a bincken da aka yi a baya, akwai yiwuwar rahoton na shida zai kasance wanda ya fi mayar da hankali kan batun rawar da mutane ke takawa wajen haddasa matsalolin sauyin yanayi.
A rahotn baya da aka fitar a 2013, marubutan sun bayyana cewa dumamar yanayin da ta fara tun a 1950 ta kasance abin da aka danganta sosai da harkokin ɗan Adam.
Mai yiwuwa kuma wannan karon za su yi amfani da kalamai masu karfi, duk da jayayyar da wasu kasashen ke yi.
Amma kuma, mai yiwuwa za a fi mayar da hankali sosai kan abin da ke faruwa a yanzu da kuma wanda zai faru nan gaba, a maimakon abubuwan da suka faru a baya.
Za a bude sabon babi kan abubuwa masu tsanani kan sauyin yanayi. Wannan zai hada da batun abubuwa masu munanan tasisri kamar guguwa da ambaliyar ruwa ko kuma fari da muka shaida a fadin duniya cikin watannin baya-bayan nan.
"Don haka za mu yi tsammanin karin wasu bayanai. Ko shakka babu, kusan a karon farko a cikin tawagar IPCC, (za mu samu) karin cikakkun bayanai game da hadarin yanayi mai tsanani,'' in ji Farfesa Corinne Le Quéré, daga Jami'ar East Anglia, da ke cikin tagawar bincike biyu na IPCC a baya.
Kamar sabbin bayanai game da fushin teku da yanayin yankin Kusurwar Arewacin Duniya mai tsananin sanyi da na Kusurwar Kudancin Duniya, takaitaccen rahoton zai samar mana da karin sabbin bayanai kan ainihin takaita karuwar yanayin zafi zuwa ma'aunin 1.5C a cikin wannan karnin.
Amma mece ce IPCC kuma me ya sa take da muhimmanci a gare ni?
A shekarar 1988 ne aka kafa kungiyar gwamnatoci kan sauyin yanayi (IPCC) don samar wa da masu mulki cikakkun bayanan binciken kimiyya kan matakan da suka dace a dauka kan matsalar sauyin yanayi bayan kowace shekara shida ko bakwai.
Yayin da duniya ta dumama a cikin shekara 30 da suka gabata, kungiyar IPCC ta kasance wata muhimmiya ga abubuwa guda uku: samar da takaitattun bayanai kan fahimtar matsalar sauyin yanayi a kimiyyance, da duba tasirin sauyin yanayi, da kuma bayar da shawarwari kan hanyoyin da za su taimaka wa rayuwar kowa.
Mutane da dama na tsammanin cewa kungiyar ta IPCC wani dandali ne na kimiyya kawai, amma wannan ba shi ne cikakken bayani game da ita ba.
"Gaskiyar magana ita ce, kungiyar IPCC ta kunshi wakilai daga gwamnatoci 195. Kuma wannan a ganina muhimmin abu ne game da IPCC. Ba wai taron masana kimiyya ba ne kawai ke samar da rahotanni; gwamnatoci ne suka saka su…. Kuma hakan ne ya sa suka fita daban,'' in ji Richard Black, wani mai kwararren mai bincike a Cibiyar Grantham da ke Kwalejin Imperial a birnin London.
"Wannan muhimmin abu ne," in ji masani kan sauyin yanayi Ed Hawkins, daga Jami'ar Reading. "Amincewa daga kalma zuwa kalma na nufin duka gwamnatocin sun bayar da goyon bayansu game da sakamakon binciken,''kamar yadda masanin ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Cikin shekarun da suka gabata, rahotannin kungiyar ta IPCC sun kasance kunshe da kalamai masu karfi a yayin da aka samar da shaidu.
A shekarar 2013, sakamakon binciken ya bayyana cewa mutane ne ''suka mamaye dalilan faruwar'' dumamar yanayi kuma kasidar ta taimaka wajen tsara hanyoyin da suka kamata a bi a yarjejeniyar Paris kan sauyin yanayi da aka rattaba wa hannu a 2015.
A shekarar 2018, IPCC ta fitar da rahoto na musamman da ke duba bangare day ana matsalar: barin yanayin zafi na duniya zuwa kasa da ma'aunin 1.5C. An kuma saka wa wannan kasida wasu nagartattun bayanai masu hankulan matasan da a shirye suke su fita kan titina su bukaci daukar matakai daga gwamnatoci.
A ranar 9 ga watan Agusta ne ake sa ran sake wallafa rahoton IPCC nag aba - kuma akwai yiwuwar zai yi gagarumin tasiri gababin babban taron zaman tattaunawa kan sauyin yanayi na COP26 a birnin Glasgow, cikin watan Nowamba mai zuwa.
"Ina ga zai kasance wata matashiya, ko shakka babu,'' in ji Farfesa Black.
Za ka iya yarda da kimiyya?
Bayan wallafa shi, rahoton binciken zai kasance sakamakon ayyukan masana fiye da 200, da aka rarraba su zuwa tawaga-tawaga don yin nazari kan bayanan da aka tattara a cikin shekaru hudu da suka gabata.
An tattauna a kan daftarin farko kuma ya samu samu ra'ayoyi 75,000 daga masu binciken.
"Masanan sun fitar da kasidar wacce wakilin Majalisar Dinkin Duniya ya kalubalanci ko wane sashenta, amma kuma masanan sun kare duka bayanansu,'' in ji Farfesa Le Quéré.
"Babu wani abu da aka rubuta da a yake da wani kuskure a kimiyyance. Don haka masana kimiyya na da 'yancin wannan ba daidai bane, kana kasidun sun kara samun tagomashi daga karshe saboda wadannan hanyoyi.'
Daya daga cikin abubuwan da suka kara wa rahoton karfi shi ne ba kasidar bincike daya ce kawai a kan wani batu ba - masu nazarin sun duba ko wane sashe na binciken da aka gudanar a ko wane bangare da ake bukata.
"Wasu lokutan kungiyar ta IPCC kan fuskanci suka kan mayar da hankali wajen sasantawa,'' in ji Dakta Emily Shuckburgh, daga Jami'ar Cambridge.
"Amma kuma kasancewa takaitaccen bayani ne a cikin ko wane bangare da shaidun da aka shata, gagarumin abu ne mai amfani.''
Wannan shi ne karon farko da IPCC ta yi yunkurin zaman tattaunawa kan amincewa daga nesa. Galibi wadannan taruka kan dauki tsawon mako guda kana ya kan kasance cikin tattaunawa mai karfi tsakanin wakilan gwamnat ia na masana kimiyya.
Yayin da watanni kadan suka rage kafin gudanar da babban taron na COP26 kan sauyin yanayi, me yiwuwa abubuwan da ke gaban mahalarta taron zai kasance mafi girma fiye da yadda aka sani a tarihin baya-bayan nan.
Idan aka yi la'akari da abkuwar bala'oi da muke shaida wa a fadin duniya, yanzu jama'a da 'yan siyasa sun waye game da batun sauyin yanayi fiye da yadda aka sani a baya.
Hakan zai kara yin matsin lamba wa kungiyar IPCC. Da alamu mahalarta taron za su bata hankalin dare nan gaba.