Jami'an tsaro sun ce sun kawo karshen garkuwa da otal da al-Shabab ta yi a Mogadishu

Jami’an tsaro a Somalia sun ce sun kawo karshen dauki-ba-dadin da suka kwashe sa’a talatin suna yi da mayakan kungiyar al-Shabab masu ikirarin jihadi wadanda suka kutsa tare da kame otal din Hayat a babban birnin kasar Mogadishu.

Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da hakan, sannan kuma babu tabbacin mutane nawa gumurzun ya yi sanadin hallakawa.

Amma wasu shedu na cewa akalla farar hula ashirin sun mutu.

Duk da cewa babu tabbacin wannan ikirarin na jami’an tsaron na Somalia na kawo karshen wannan mummunan artabu da ya janyo asarar rayukan musamman farar hula da hukumomi ba su kai ga fitar da alkalumansu ba, amma abin da ya bayyana a fili shi ne yadda aka yi kaca-kaca da ginin otal din sakamakon barin wutar da jami’an tsaron suka yi ta amfani da manyan makamai.

Wasu kafofi na cewa farar hulha akalla talatin ne lamarin ya yi sanadiyyar salwantar rayukansu ciki har da mai otal din.

Tun ranar Asabar wani jami’in tsaro ya gaya wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, zuwa lokacin sun tabbatar da mutuwar mutum goma sha biyu yawanci farar hula.

Hukumomin wani asibiti da aka kai wadanda suka tsira da rai sun ce akwai akalla mutum arba’in da suke yi wa magani wadanda aka raunata a farmakin, da kuma wasu da wani harin makami da aka harba a wani sashen birnin na Mogadishu ya illata.

Jami’an tsaron sun kwashe sa’o’I suna kokarin shiga benen ginin, saboda ‚yan bindigar sun yi amfani da bam suka tarwatsa matattakalar.

Wurin dai ya kasance daya daga cikin inda jami’an gwamnatin Somalia ke taruwa.

Bayanai sun ce tun a ranar Juma’a da daddare ne maharan suka kai harin, inda suka yi amfani da bama-bamai na mota har biyu a harin.

Mota ta farko sun tayar da bam din da ke cikinta ne wajen kawar da shingen tunkarar otal din.

Yayin da suka yi amfani da ta biyun wajen fasa kofar ginin sannan suka kama ginin, tare da garkuwa da mutane a ciki.

Bayan da suka kama otal din ne kungiyar ta fitar da wata sanarwa inda ta ce, maharan za su harbe dukkanin mutanen da ke ciki.

Shekara goma sha biyar ke nan kungiyar ta al-Shabab na tayar da kayar baya ga kwarya-kwaryar gwamnatin kasar ta Somalia.

Kungiyar mai alaka da al-Qaeda, na iko da yawancin sassan kudanci da tsakiyar kasar ta Somalia, a yanzu ma har ta kai ga tasiri a wasu yankunan gwamnati ke iko da su a babban birnin kasar Mogadishu.

Harin na ranar Juma’a shi ne na farko a babban birnin tun bayan zaben sabon shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud a watan Mayu.